Yan bindiga
Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi, ya nuna bacin ransa kan daganta 'yan bindiga da addinin musulunci. Basaraken ya bayyana cewa babu musulunci a tattare da su.
Rahotanni sun ce an kashe fitaccen shugaban 'yan bindiga Kachalla Sani Yellow a Anka, amma ana samun sabanin bayanai kan yadda mutuwarsa ta faru.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta tabbatat da cewa wasu jami'anta ke rakiyar gawar abokin aikinsu zuwa gida sun fada tarkon 'yan bindiga a jihar Kogi.
Kungiyar Coalition of Northern Groups (CNG) ta soki gwamnatin jihar Katsina kan tsare Dr. Bashir Kurfi. Ta bayyana cewa 'yan bindiga ya kamata a rika yaka.
Murna da barke da aka samu rahoton ceto dalibai da malaman da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Oyo. Sun kwashe fiye da kwanaki 50 a tsare.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a wani yanki na babban birnin tarayya Abuja. 'Yan bindigan sun kashe wani jami'in tsaro.
Dattawan Katsina da kungiyoyi daban-daban na neman lallai jami'an tsaro su saki Dr. Bashir Kurfi bayan kama shi da zarginsa da yin kalaman bata sunan gwamnati.
Dakarun rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Osun sun harbe wasu 'yan bindiga 2 da ake zargi sun yi garkuwa da wani mutum. An kwato bindiga a hannunsu.
Dakarun sojojin Najeriya tare da sauran jami'an tsaro sun kashe 'yan ta'adda takwas a Bakori, sun kuma kwato bindigogi AK-47 biyu da babura biyar.
Yan bindiga
Samu kari