Yan bindiga
Tsohon Ministan Tsaro Mohammed Badaru ya karyata rahoton bogi da ya ce ya yi murabus ne saboda zargin hare-haren Amurka da gwamnatin Tinubu kan ‘yan daji.
'Yan bindiga sun sace wasu dalibai biyar a jami'ar RSU da ke jihar Rivers. 'Yan ta'addan sun afka dakunan kwanan daliban ne sun sace su cikin dare.
Shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya ce matsalar rashin tsaro ta sa sun hada kai bisa ganin uwar bari bayan ji a jika.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ziyarci wasu kananan hukumomin Kano da ke fama da barazanar 'yan bindiga. Ya gana da jami'an tsaro da jama'ar yankunan.
Yan sandan babban binrin tarayya sun kashe ’yan bindiga uku, sun kama babban dan ta'adda, kuma sun dakile mugun shirin garkuwa da mutane a Abuja.
Gwamnatin Abia ta karyata labarin da ake yadawa cewa Gwamna Alex Otti ya sha da kyar a harin yan bindiga, ta ce wadanda aka farmaki ba ayarin Gwamna ba ne.
Dakarun Najeriya sun bayyana nasarorin da suka samu sun kashe 'yan ta'adda takwas da kama 51 tare da kama makamai a farmakin da suka kai cikin kwana uku.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da manoman da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Kaduna. Sun tafi da su zuwa cikin daji.
Mai taimakawa shugaban kasa game da harkokin tsaro ya ce Najeriya na samun tallafi daga Amurka, Faransa, Birtaniya da wasu kasashe a yaki da ta'addanci.
Yan bindiga
Samu kari