Jihar Enugu
Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan wasu 'yan ta'addar IPOB a wajen da suke tsafi, an kashe da dama. Sojojin sun kashe wasu masu garkuwa da mutane a Enugu.
Shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamntin Tinubu ta shirya taimakon 'yan kasa. Ya ce akwai shiri na musamman a kan wutar lantarki don bunkasa cinikayya.
Farashin shinkafar gida ya ragu da kashi 10 a Enugu; wanda ya sanya mutane farin ciki gabanin Kirsimeti, yayin da dillalai ke ba da shawarar saye kafin ta kara kudi.
Shugaban Isi-Uzo ya gabatar da kasafin Naira biliyan 5.5 don 2025. Ayyuka sun haɗa da tituna, lafiya, aikin gona, ICT da shirin Gwamna Mbah na Smart Green Schools.
Ciyaman na ƙaramar hukumar Igbo Ekititi. Eric Odo ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta fara bai wa matan da suka rasa mazajensu alawus a kowane wata.
Wasu 'yan bindiga sun tare hanya tare da yin garkuwa da wani limamin cocin Katolika a jihar Enugu. An fara kira ga jama'a da su yi adduo'i domin ganin ya kubuta.
Yan kwadago sun tabbatar da cewa tun a Nuwamba, 2024, ma'aikata suka fara ganin sabon mafi ƙarancin albashi, sai dai ba a aiwatar da shi yadda ya dace ba.
Babbar kotun jihar Enugu ta yanke hukunci a karar da wani mutumi ya shigar kimanin shekara 10 da ta wuce, ta umarci gwamnati ta biya shi diyyar N55m.
Shugaban karamar hukumar Igbo Etiti, Hon. Eric Odo ya ba wasu hadimansa guda biyu na musamman masu kula da bangaren doya da yalo da kuma barkono.
Jihar Enugu
Samu kari