
Zaben Shugaban kasan Najeriya







Yayin da ƴan adawa ke shirye shiryen haɗewa domin kayar da Bola Tinubu, wata kungiyar siyasa ta nemi hukumar zaɓe INEC ta yi mata rijistar zama jam'iyyar siyasa.

Wasu daga cikin jagoroi a jam'iyyar PDP sun bayyana shirinsu na shiga hadakar da za ta taimaka wajen korar Bola Tinubu daga shugabancin Najeriya.

Shugaban NNPP na jihar Ondo, Peter Olagookun ya bukaci Atiku Abubakar da sauran ƴan adawa su marawa Rabiu Musa Kwankwaso baya a zaɓen 2027 mai zuwa.

Atiku ya musanta karbar kudi daga Sanwo-Olu, yana mai cewa zargin karya ne. Tawagarsa ta bukaci EFCC ta bayyana bincikenta, domin dakile makircin 'yan siyasa.

Wani rahoto ya nuna cewa ana shirin nada sabon shugaban hukumar INEC da zai zama dan amshin Shatar gwamnatin Tinubu don samun damar magudin zabe a 2027.

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya yi martani kan kalaman da Atiku Abubakar ya yi na cewa bai yi nadamar kin daukarsa a matsayin mataimaki ba a 2023.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar SDP, Adewole Adebayo ya bayyana cewa salon mulkin Bola Ahmed Tinubu abin kunya ne, ganin halin da jama'a ke ciki.

Majalisar wakilai ta yi karatu na biyu wa kudirin mayar da zaben gwamnoni da shugaban kasa rana 1 a Najeriya. Ana sa ran za a fara aiki da shi a 2027.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa mahar da ƴan adawa za su haɗa za ta fitar da mutum ɗaya da zai gwabza da Tinubu.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari