Jihar Edo
Fusatattun matasa sun korar 'yan kasuwar Hausawa a Ekpoma, Gwamna Okpebholo ya yi Allah-wadai da harin. 'Yan sanda sun ceto mutane tara daga masu garkuwa.
Dan majaliaar wakilai daga jihar Edo, Hon. Murphy Osaro Omoruyi ya sauya sheka daga LP zuwa ADC, ya ce lokaci ya yi da zai bar cikin rikicin jam'iyyar.
Gwamna Monday Okpebholo ya biya ma'aikatan Edo albashin watan 13, lamarin da ya sa ma'aikata suka yaba masa domin zai taimaka musu wajen biyan kudin makarantar yara.
'Yan daba sun yi wa dan uwan tsohon gwamna tsirara, sun kuma lakada masa duka bisa zargin yana batanci ga mai martaba sarkin Benin. Godwin Obaseki ya yi martani.
Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Edo, Charles Idahosa wanda kuma jigo ne jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ya rasu yana da shekaru 72 a duniya.
Tsohon gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana cewa shugabannin da ke cin amanar da Allah ya ba su, za su dandana kudarsu a wurin Ubangiji ranar Lahira.
Wata tankar man fetur ta yi hadari a Auchi jihar Edo. Wuta ta tashi kuma jama'a da dama sun jikkata bayan fetur ya kwalala zuwa gidaje da shaguna.
Sanata Adams Oshiomhole ya ce ya yi murnar murabus din shugabannin NMDPRA da NUPRC, yana mai cewa hakan ya zama dole domin ceto tattalin arzikin Najeriya.
A labarin nan, za a ji yadda wani matashi ya rasa rayuwarsa a garin tseren motoci domin murnar kammala jarrabawa a wata jami'a da ke jihar Edo a ranar Litinin.
Jihar Edo
Samu kari