Zaben Edo
A ranar 21 ga watan Satumba, 2024 INEC ta tsara gudanar da zaɓen gwamna a jihar Edo, mun tattaro muku ƴan takara 3 na sahun gaba da za su kata a zaɓen.
Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Edo, jam'iyyar PDP da babban sifetan yan sanda, Kayode Egbetokun suna zargin juna kan zaben da a yi a wannan wata.
A cikin wannan labarin za ku ji cewa awanni biyu kacal kafin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben gwamnan Edo, APC ta janye daga shirin.
Shugaban kungiyar NLC a Edo, Odion Olaye ya sake rura wutar rikici yayin da ake shirin gudanar da zaben jihar a ranar 21 ga watan Satumbar 2024 da muke ciki.
Kotun daukaka ta zartar da hukunci kan karar da ke neman soke tikitin takarar gwamna na Barista Olumide Akpata karkashin inuwar jam'iyyar Labour Party.
Yayin da ake shirin zaben jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya ki amincewa da sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya kan zaben da ke tafe nan da kwanaki tara.
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yi zargin cewa ana shirin cafke magoya bayan jam'iyyar PDP gabanin zaben gwamnan jihar da ke tafe nan da kwanaki masu zuwa.
Ana shirin gudanar da zaben gwamnan jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya yi babban rashi bayan hadimansa guda hudu sun yi murabus tare da watsar da PDP.
Tsohon dan majalisar dokokin jihar Edo, Honarabul Emmanuel Agbaje ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP. Ya sauya shekar ne bayan ya fice daga jam'iyyar APC.
Zaben Edo
Samu kari