Zaben Edo
Zababben gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya nada Fred Itua a matsayin Babban Sakataren Yada Labarai don inganta sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.
Rikicin siyasa ya kara tsami da Gwamna mai jiran gado, Sanata Monday Okpebholo ya yi zargin cewa ana neman Gwamna Godwin Obaseki an rasa a jihar.
Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya rusa majalisar zartarwa da sauran masu mukamai a gwamnatinsa yayin da yake kwanakin karshe na wa'adinsa na biyu a matsayin gwamna.
Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya bayyana cewa yana da yaƙinin cewa ya zarce alƙawurran da ya ɗaukarwa mutane a lokacin yakin neman zabe a 2016.
Zababben gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya koka kan yadda gwamnatin Hodwin Obaseki ke ci gaba da karbo basussuka yayin da ake shirin mika masa mulki.
Olumide Akpata, dan takarar Labour a zaben gwamnan Edo a 2024, ya bayyana matakin da ya dauka na kin kalubalantar sakamakon zaben da aka kammala kwanan nan a kotun.
Wasu tulin magoya bayan jam'iyyar PDP sun fita zanga-zanga a babban ofishin hukumar zaɓe INEC na jihar Edo, sun bukaci a soke sakamakon zaɓen gwamna.
Kungiyar SERAP ta bukaci shugaban hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu da ya binciki zarge-zargen rashawa da laifuffukan zabe tsakanin gwamnoni da mataimakansu.
Sanata Orji Kalu ya karyata cewa ya rasu a kasar Amurka. Ya kuma taya APC murna kan samun nasara a zaben Edo. Sanatan ya kara da cewa ana wahala a Najeriya.
Zaben Edo
Samu kari