Matsin tattalin arziki
Lauyan kare hakkin ɗan adam, Femi Falana, ya ce cire tallafin mai da Shugaba Tinubu ya yi babban kuskure ne na tattalin arziki, wanda ya janyo wa yan Najeriya ƙunci.
Bincike ya nuna cewa, zai ɗauki ma'aikaci mai karɓar mafi ƙarancin albashi na N70,000 fiye da shekaru biyu kafin ya iya mallakar sabuwar wayar iPhone 17.
Yan gwagwarmaya a Arewacin Najeriya da suka hada da Abba Hikima da Dan Bello sun shirya daukar mataki kan gwamnatin Bola Tinubu a Najeria kan basukan N-Power.
Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa bude boda domin shigo da kayan abinci ya karya farashin abinci a Najeriya, ya ce an karfafi manoma.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya gayyaci kungiyar 'yan bola jari gidan gwamnati kan yawan sata a jihar. Ya bukaci a daina satar kayan gwamnati da na jama'a.
Jihohi 31 sun tara wa kansu bashin N2.57tr amma ba su iya jawo jarin waje a zangon farko na 2025 ba; jihohi 10 kadai sun karbo bashin N417bn duk da karin FAAC.
Dokar haraji da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanyawa hannu za ta wajabta wa 'yan kasa amfani da rajistar haraji kafin mu'amala da banki daga shekarar 2026.
Gwamnatin tarayya ta yi karin haske game da harajin fetur na 5% da aka sanya a cikin sababbin dokokin haraji da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kawo.
Shugaban kwamitin gyaran haraji na shugaban kasa, Taiwo Oyedele ya ce sabon tsarin haraji zai saukaka wa yan Najeriya, ya fadi yadda kowa zai gano.
Matsin tattalin arziki
Samu kari