
Hukumar EFCC







Wata babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja ta yi fatali da bukatar neman beli da tsohon shugaban hukumar Inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Usman Yusuf, ya nema.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya gargadi shugaba Bola Tinubu kan kama mutane saboda siyasa bayan EFCC ta kama Ferfesa Yusuf Usman na hukumar NHIS.

Dakarun hukumar yaki da rashawa watau EFCC sun kai samame gidan tsohon shugaban NHIS, Farfesa Usman Yusuf, sun kama shi a gidansa da ke birnin Abuja.

Babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta ci gaba da sauraron shari'ar almundahana da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta shigar gabanta.

Tsohon ministan makamashi, Saleh Mamman na tsaka mao wuya, wanai ɗan canji ya ba da shaida a kansa, ya faɗi yadda suka yi harkallar canjin Daloli na N22bn.

Wasu ƴan damfarar yanar gizo da aka fi sani da Yahoo Boys sun far wa dakarun hukumar EFCC ba zato ba tsammani, sun kashe jami'i ɗaya wani na kwance a asibiti.

Hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa a Najeriya watau EFCC ta fara titsiye sarakunan da ke zaben sabon Alaafin na Oyo kan zargin karɓar rashawa.

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa watau EFCC ta cafke jami'an gwamnatin Katsina 5 bisa zargin karkatar da kimanin N.1.3bn.

Kotu da ke zamanta a Legas ta ce ta na hurumin sauraron tuhume-tuhumen da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta shigar a kan Emefiele.
Hukumar EFCC
Samu kari