Cikakken Bincike
Gwamna Dauda Lawal ya musanta naɗa wanda ake zargi da hannu a ayyukan ta'addancin ƴan bindiga, Bashir Haɗeija a wani muƙamin gwamnatin jihar Zamfara.
Jafaru Sani ya tona yadda Uba Sani yake kaddamar da ayyukan da Nasir El-Rufai ya yi duk da su na kukan ba su san inda aka kai bashin da El-Rufai ya ci ba.
Babbar kotun Kano ta sanya ranar 11 ga watan Yuli 2024 domin fara zaman sauraron karar da Kwankwaso da wasu mutane 7 suka shigar da hukumar yaƙi da cin hanci EFCC.
Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya dakatar da kwamishinar lafiya daga aiki bisa zargin rashin gaskiya da almundahanar kuɗaɗe.
Tun bayan zargin cewa mutuwar mawaƙi Mohbad ba ta Allah ba ce, gwamnati ta dora alhakin binciko dalilin mutuwar a wuyan asibitin koyarwa na jihar Lagos, (LASUTH).
Kungiya mai yaki da cin hanci da rashawa (NACAT) ta bukaci hukumar EFCC ta binciki tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa bisa zargin rashawa.
Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin da zai binciki dalilin da ya janyo daliban makarantun sakandiren jihar nan suka yi mummunar faduwa a jarrabawar 'qualifying'.
Hukumar EFCC ta bayyana sababbin hanyoyi da 'yan yahoo suka kirkiro domin damfarar mutane. Babban daraktan hukumar ne Effa Okim ya bayyana haka a jihar Edo.
Ɗan Majalisar Wakilai, Dominic Okafor ya musanta zargin da ake yi masa cewa ya nemi na goro daga kamfanin Binance inda ya ce zai dauki matakin shari'a.
Cikakken Bincike
Samu kari