Jihar Benue
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka a jihar Benue yayin ziyarar da ya shirya kai wa. Shugaban kasan ya isa jihar ne a ranar Laraba, 18 ga watan Yunin 2025.
Gwamnatin jihar Benue ta ba da hutu domin ziyarar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai jihar. Ta ce ziyarar na da matukar muhimmanci sosai.
Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a majalisar dattawan Najeriya, Seriake Dickson, ya bayyana gibin shugabanci a matakin kananan hukumomi na rura sashin tsaro.
Peter Obi ya ce Bola tinubu ya yi abin da ya dace kan matakin kai ziyara jihar Benue. Obi ya bukaci Tinubu ya ziyarci garin Mokwa na jihar Neja saboda ambaliya.
Gwamna Alia ya tattauna da Tinubu da Akume kan rikicin Binuwai. An nemi sulhu don dakatar da kisan gilla da mayar da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.
A wannan labarin, za a ji cewa bayan ya sha suka daga 'yan adawa, shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa zai ziyarci mutabeb Binuwai a ranar Laraba.
Benue na fuskantar hare-haren 'yan bindiga; sama da 100 sun mutu, dubbai sun rasa matsuguni. NEMA na neman agaji yayin da aka kafa sansanin 'yan gudun hijira.
Babban sufetan ƴan sanda na ƙasa, Kayode Egbetokun, ya isa jihar Benuwai, ya tura dakaru na musamman domin daƙile hare-haren da makiyaya ke kai wa.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi magana kan hare-haren ta'addanci da ake kai a jihar. Ya ce makiyaya dauke da makamai marasa shanu ke kai hare-haren.
Jihar Benue
Samu kari