Fashi da makami
A labarin nan, za a ji cewa masana tsaro na sauran mazauna jihar Kano sun bayyana fargaba a kan yadda lamarin fashin waya ke kara kamari da daukar rayuka.
Wani matashi dan fizge ya fada kogin Asa a Ilorin ya mutu bayan sace jakar wata mata a Ilorin na jihar Kwara. Matashin ya fada kogin ne ana kokarin kama shi.
'Yan daba sun kai hari tashar saukar jirgi da ke cikin kamfanin siminti na Ashaka da ke a Gombe. Jami'in NSCDC ya samu nasarar kashe ɗaya daga cikin 'yan daban.
Mai ba gwamnan Delta shawara kan harkokin kungiyoyin fararen hula da matasa, Harrison Gwamnishu ya yi murabus kan karuwar matsalar tsaro a jihar.
Rundunar yan sandan jihar Anambra ta bayyana cewa an cafke wani mutum mai shekaru 49 da ake zargi da hallaka mahaifiyarsa saboda sabani a kan kudin kasuwancin rogo.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana ta sanar da cewa ta samu nasarar gano wata kungiya da ke safarar mugayen makaman da ake kera wa a cikin kasar a jihar Kano.
Sheikh Isa Ali Pantami ya kubuta daga sharrin 'yan fashi a 1993 bayan sun masa harbi guda uku a hanyar Maiduguri saboda addu'a. Ya fadi yadda ya tsira a jirgin sama.
'Yan fashi da makami sun kai hari makarantar sakandare ta Yashe a karamar hukumar Kusada a jihar Katsina. Sun kashe mai gadi a lokacin da ake suhur.
Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Legas ta kama mutane 35 da ake zargi da fashi da makami. 'Yan sandan sun bayyana cewa an gurfanar da su a kotu.
Fashi da makami
Samu kari