Arewa
Rundunar sojin saman Najeriya ta dage kan cewa ba ta kai hari kan fararen hula a jihar Kaduna ba. Rundunar ta ce 'yan bindiga ta farmaka kuma ta samu nasara.
Wata kungiyar dattawan Arewa maso yamma ta gargadi Bola Tinubu kan sauya ministocin tsaro, gidaje da kasafin kudi. kungiyar ta ce ministocin sun yi kokari.
A wani harin kwantan bauna na ramuwar gayya, yaran marigayi Kachalla Nagala sun halaka hatsabibin dan bindiga, Kachalla Mai Shayi da ke dabar Kachalla Mai Bille.
Gwamnatin jihar Bauchi ta ware kudi domin gyara tare da inganta fadojojin sarakunan gundumomi 11 na karamar hukumar Dass da ke a jihar. Mun zanta da Muslim Dabo.
Rundunar sojin Najeriya ta samu nasara kan yan ta'adda a jihohin Arewacin Najeriya. Sojoji sun kashe yan ta'adda da dama sun ceto mutanen da aka sace.
Rundunar yan sanda a jihohin Arewa da Kudu sun yishiri domin magance masu tayar da fitina a lokacin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a watan Oktoba.
Ana fargabar mutane hudu da suka hada da wata mai shayarwa sun mutu a Gusau, jihar Zamfara bayan da wata motar tirela ta murkushe su a lokacin da suke kan babura.
Sanatoci sun tafka zazzafar muhawara a lokacin sake duba kundin tsarin mulkin kasar na 1999 inda wasu ke ba da ra'ayin komawa mulkin yankin, wasu kuma na adawa.
Tsohon gwamnan jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame ya tafka babban rashi bayan mutuwar mahaifiyarsa a daren ranar Asabar 28 ga watan Satumbar 2024.
Arewa
Samu kari