Arewa
Kotun Majistare a jihar Kano ta umarci ci gaba da tsare Hafsat Surajo a gidan kaso kan zargin hallaka wani matashi mai suna Nafi'u Hafizu a jihar Kano.
Gwamnatin jihar Niger ta sanar da haramcin sha da sayar da barasa a wasu kananan hukumomi tara na jihar, ciki har da Suleja. Za a tashi gidajen giya daga Minna.
Jagoran siyasar jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci wata addu'a ta musamman kan hukuncin Kotun Koli da neman nasarar Gwamna Abba Kabir.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta raba kayayyaki masu tarin yawa ga 'yan mazabarta don gudanar da bikin Kirsimeti.
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya bayyana cewa ya na da tabbacin samun nasara a Kotun Koli yayin da ake dakon hukuncin kotun kan shari'ar zaben gwamnan jihar.
Hon. Nwuchiola Ojoma Comfort ta kafa tarihin zama mataimakiyar kakakin Majalisar jihar Kogi bayan murabus din Hon. Enema Paul daga kujerar a ranar Alhamis.
Gwamna Yahaya Bello ya gwangwaje 'yan Majalisar jihar da motocin alfarma guda 40 da kuma manyan motoci guda hudu ga alkalan jihar kan gudunmawar da suka bayar.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bai wa tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega mukamin uban Jami'ar jihar da ke karamar hukumar Keffi.
Tsohon kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Yakubu Dogara ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa, Mama Saratu Yakubu Tukur ta na da shekaru 103 a duniya.
Arewa
Samu kari