Arewa
Wani bidiyo da yan jaridu suka gani ya tabbatar da kashe ‘yan ta’adda da lalata maboyarsu a Sokoto, yayin hare-haren sama na Amurka a ƙarshen Disambar 2025.
Gwamnatin Taraba ta rufe babban asibitin ƙwararru na Jalingo don gyare-gyare; marasa lafiya masu jinyar ƙoda sun shiga tashin hankali sakamakon rashin wurin jinya.
Kungiyar NADECO USA ta roki Shugaba Tinubu ya sallami Ministan Abuja, Nyesom Wike, don kawo ƙarshen rikicin siyasa a Jihar Rivers kafin zaɓen 2027.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Sarkin Kagarko a jihar Kaduna, Alhaji Sa’ad Abubakar, bayan fama da jinya, inda ya rasu a yau Alhamis 8 ga watan Janairun 2026.
Yara 469 ne suka mutu a Kano sakamakon rashin abinci mai gina jiki a 2025; UNICEF ta bayyana cewa kashi 51.9% na yara a jihar suna fama da matsalar tsumburewar jiki.
An gano wani babban makami mai linzami a yankin Mashegu na jihar Neja wanda ake zargin na Amurka ne; jami’an tsaro sun kwashe makamin zuwa Minna a yau don bincike.
Kungiyar dattawan Arewa, ACF ta bayyana cewa ba za ta goyi bayan kowane dan takarar shugaban kasa ba a 2027, amma za ta tattauna da su kan tsaro, talauci, da ilimi.
Gwamnatin jihar Bauchi ta bukaci sababbin hakiman da su maida hankali wajen inganta rayuwar jama'ar da suke jagoranta, tuni aka raba masu takardun fara aiki.
Mazauna Borgu da Agwara a jihar Niger na tserewa gidajensu bayan kisan mutane fiye da 40; sun koka kan janyewar sojoji yayin da ’yan bindiga ke yi musu barazana.
Arewa
Samu kari