Arewa
Kungiyar NADECO USA ta roki Shugaba Tinubu ya sallami Ministan Abuja, Nyesom Wike, don kawo ƙarshen rikicin siyasa a Jihar Rivers kafin zaɓen 2027.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Sarkin Kagarko a jihar Kaduna, Alhaji Sa’ad Abubakar, bayan fama da jinya, inda ya rasu a yau Alhamis 8 ga watan Janairun 2026.
Yara 469 ne suka mutu a Kano sakamakon rashin abinci mai gina jiki a 2025; UNICEF ta bayyana cewa kashi 51.9% na yara a jihar suna fama da matsalar tsumburewar jiki.
An gano wani babban makami mai linzami a yankin Mashegu na jihar Neja wanda ake zargin na Amurka ne; jami’an tsaro sun kwashe makamin zuwa Minna a yau don bincike.
Kungiyar dattawan Arewa, ACF ta bayyana cewa ba za ta goyi bayan kowane dan takarar shugaban kasa ba a 2027, amma za ta tattauna da su kan tsaro, talauci, da ilimi.
Gwamnatin jihar Bauchi ta bukaci sababbin hakiman da su maida hankali wajen inganta rayuwar jama'ar da suke jagoranta, tuni aka raba masu takardun fara aiki.
Mazauna Borgu da Agwara a jihar Niger na tserewa gidajensu bayan kisan mutane fiye da 40; sun koka kan janyewar sojoji yayin da ’yan bindiga ke yi musu barazana.
Yara 11 sun tsinci harsasan kakkabo jiragen sama a magudanar ruwa a Maiduguri; sojoji sun killace yankin yayin da aka bai wa yaran kyautar kuɗi saboda jarumta.
Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da kisan mutum 30 a kasuwar jihar Niger, tare da jajantawa jihar Yobe kan haɗarin jirgin ruwa da ya kashe mutane 25.
Arewa
Samu kari