Akwa Ibom
Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom da Rivers a mulkin soja, Manjo-janar Godwin Osagie Abbe ya riga mu gidan gaskiya a jiya Asabar 21 ga watan Disambar 2024.
Domin rage zaman kashe wando, gwamnan jihar Akwa Ibom ya raba jalin N50,000 ga matasa akalla 15,000 a faɗin kananan hukumomi 31, ya ce zai faɗaɗa shirin.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya bayyana cewa ba zai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin N80,000 ba har sai an gama tantance ma'aikata.
Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya janye kansa daga yarjejejniyar da suka yi da kungiyar NLC kan albashi inda ya ce sai ya gama tantance ma'aikata.
Hadimin Sanata Godswill Akpabio mai suna Uduak Udo ya nemi yafiyar Gwamna Umo Eno kan kuskuren taya shi murnar mutuwar matarsa wacce ta rasu a watan Satumbar 2024.
yan sanda a jihar Akwa Ibom sun kashe yan bindiga uku cikin wadanda suka sace daraktan ma'aikatar shari'a suka daure shi a cikin wani rami da 'yar uwarsa.
Rundunar 'yan sandan jihar Akwa Ibom, ta samu nasarar bankado wata masana'antar kera bindigogi. Ta cafke daga cikin mutanen da ake zargi kan lamarin.
Malamin jami'ar Uyo, Inih Ebong ya samu nasara a kotu bayan fafutkar shekaru 22 yana zuwa kotuna. Kotu ta umarci a biya shi hakkokinsa na shekarun.
Yan kwadago sun fasa shiga yajin aikin da suka yi niyya bayan Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya amince da N80,000 a sabon mafi ƙarancin albashi.
Akwa Ibom
Samu kari