Aikin Hajji
Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu mabiya addinin Katolika masu goyon bayan auren jinsi 1,400 daga ƙasashe 20 sun gudanar da taron ziyara na musamman a Vatican.
A labarin nan, za a ji cewa wata baiwar Allah mai suna Maryam Hussaini Abdullahi ta gamu da iftila'in alakanta jakarta da tulin wiwi a kasar Saudiyya.
Hukumar EFCC mai yaki da rashawa ta tsare wasu manyan jami'an hukumar Hajji ta kasa, NAHCON bisa zargin almundahana a Hajjin shekarar 2025 da aka yi.
Hukumar NAHCON ta fara shirin Hajjin 2026 tun da wuri, ta ce kujeru 95,000 aka samu daga Saudiyya, inda kudin ajiya ga maniyyata ya fara daga ₦8.5m kacal.
Hukumar Hajji ta Najeriya watau NAHCON ta bayyana cewa cunkoson jiragem sama a filayem jirgin Saudiyya sun kawo tsaiko a aikin jigilar alhazai zuwa gida.
Hukumomin da ke kula da harkokin sufurin jiragen sama a Indonesia sun canza wa wani jirgin alhazai wurin sauka bayan samun saƙon barazanar bam a ciki.
Wasu daga cikin jihohin Najeriya sun ba da tallafi ga Alhazansu da ke kasa mai tsarki. An ba da tallafin ne domin saukakawa Alhazan yayin gudanar da aikin Hajji.
NAHCON ta kula da alhazai 13 masu tabin hankali da mata 3 da suka yi barin ciki a aikin Hajji. Dr. Garba ya bayyana kalubalen samun magunguna a Saudiyya.
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya gwangwaje Alhazan jihar da kyauta mai tsoka a kasa mao tsarki. Ya ba su kudade domin yin guzuri zuwa gida.
Aikin Hajji
Samu kari