Aikin Hajji
Hukumomi a kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa wata mata mai suna Hajiya Hawawu daga Kwara ta rasu, binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa ta yi ajalin kanta.
Gwamnatin jihar Kano ta samar da asibiti a kasa mai tsarki domin duba Alhazan jihar masu gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2024 a Saudiyya.
Kungiyar Concerned South-South Muslims da ke Kudu maso Kudu ta bukaci Bola Tinubu kan sauya sunan wakiliyar hukumar NAHCON a yankin, Zainab Musa.
Maniyyatan aikin hajjin bana daga jihar kwara sun yi zanga saboda sauke rashin tashi da su da zuwa kasa mai tsarki domin sauke farali. Gwamnati ta ba su hakuri.
Gwamnatin jihar Kano ta ƙara ɗaukar matakai da nufin inganta walwala da jin daɗin alhazan jihar na tsawom lokacin da za su ɗauka a ƙasa mai tsarki.
Allah ya yiwa wata Hajiya 'yar Najeriya a birnin Madina yayin gudanar da aikin Hajji. Hajiyar wacce ta fito daga Neja ta rasu ne bayan ta kamu da rashin lafiya.
Jami'an tsaro na musamman sun kama gungun yan damafara masu cutar mutane da sunan sama musu izinin aikin Hajji a Makka. An kama su da abubuwa da dama.
NDLEA ta kai samame a otal din Emerald dake unguwar Ladipo a jihar Legas inda aka kama wasu alhazan Najeriya suna kokarin hadiye hodar iblis gabanin tashinsu.
Mahukunta a kasar Saudi Arabia sun roki ɗaukacin musulmai na ƙasa su fara fita duban jinjirin watan Babbar Sallah daga gobe Alhamis, 29 ga watan Dhul Qa'adah, 1445H.
Aikin Hajji
Samu kari