Abun Bakin Ciki
Barayi sun haura katanga, sun sace akuyar Kirsimet a Gwagwalada da ke Abuja. Mai akuyar ya kai rahoto yayin da ‘yan sanda suka soma bincike don gano barayin akuyar.
Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa FRSC ta tabbatar da mutuwar mutum uku, wasu huɗu sun jikkata a wani hatsarin da ya rutsa da ɗan adaidaita sahu a jihar Jos.
Jirgin kasa ya murkushe mota dauke da buhunan shinkafa a yankin Iju-Fagba, jihar Legas. Jama’a sun koka kan rashin shingen tsaro da alamar isowar jirgi.
Tsohon mataimakin sufetan rundunar ƴan sanda na ƙasa, Bola Longe ya riga mu gidan gaskiya, ya rasu ne ranar Lahadi da ta gabata bayan fama da jinya.
Bayan mutuwar wani matashi a hannun yan sanda, Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bukaci rundunar ta binciki mutuwar Jimoh AbdulQodir a hannun jami'ansu.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi rashin tsohon hadiminsa, Hon. Shima Ayati wanda ya rasu a Makurdi bayan gajeriyar rashin lafiya.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi alhini kan rasuwar Mai Shari’a Uthman Argungu inda ya yaba gudunmawarsa ga kasa, tare da yin addu’ar Allah ya jikansa.
'Yan sanda sun kama mutum 15 kan zargin sun kone makaranta da ofishin CJTF a Bauchi; kwamishinan ‘yan sanda ya umurci cikakken bincike kan lamarin.
Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom da Rivers a mulkin soja, Manjo-janar Godwin Osagie Abbe ya riga mu gidan gaskiya a jiya Asabar 21 ga watan Disambar 2024.
Abun Bakin Ciki
Samu kari