Abun Bakin Ciki
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nuna takaici bayan aukuwar iftila'in da ya yi sanadin mutuwar mutane a Abuja da Anambra inda ya fasa gudanar da bukukuwan ya shirya.
Mutum 27 sun mutu a turereniya yayin rabon shinkafa a Okija, Anambra. Ganau sun bayyana yadda kyakkyawan niyya ya koma masifa, bayan mutane sun rasa rayuka.
Rundunar ƴan sanda ta tabatar da nutuwar ɗaliban Jami'ar OOU 3 a wani mummunan hatsarin mota da ya afku jiya Juma'a, wasu mutum 2 na kwance a asibiti.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar yara bakwai da wasu mutane uku yayin turereniya domin samun kayan tallafi saboda halin kunci a wani coci a Abuja.
Kotun Abuja ta tsare Olamide Thomas kan tuhume-tuhume uku da suka shafi barazana ga dan shugaban kasa. An dage shari’ar zuwa 30 ga Disamba don ci gaba.
Rahotannin da ke shigo mana daga jihar Oyo sun nuna cewa an tafka asarar makudan kuɗi a gobarar da ta tashi a kasuwar sayar da kayan gayarn ababen hawa.
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta umarci kamfanin sadarwa na MTN ya biya diyyar N15m ga wani abokin huldarsa kan cire masa kudi ba tare ya yi rijista ba
Wasu jami'an ƴan sanda uku da matar da ake zargi da aikata laifi sun gamu da ajalinsu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a jihar Ondo.
Hukumar ƴan sandan jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar wani jami'in tsaro mai zaman kansa bayan ya yanke jiki ya faɗi a bakin aiki, an fara gudanar da bincike.
Abun Bakin Ciki
Samu kari