Abun Bakin Ciki
Rahotanni sun bayyana cewa wani DPO na yan sanda a jihar Legas ya yanke jiki ya faɗi a ofis, Allah ya masa rasuwa tun kafin a ƙarisa asibiti ranar Alhamis.
Fusatattun daliban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Lafiya da ke Jega a Jihar Kebbi sun kona gidan shugaban makarantar Haruna Saidu-Sauwa tare da lalata motarsa.
Hukumomin Najeriya sun yi gaggawar mayar da martani bayan da wata mota mai amfani da gas din CNG ta fashe a wani gidan mai da ke garin Benin na jihar Edo.
Tsohon Ministan yada labarai, Jerry Gana ya yi jimamin mutuwar Sanata a Najeriya, Jonathan Zwingina wanda ya rasu a farkon watan Oktoban 2024 da ta gabata.
A yau Laraba 16 ga watan Oktoban 2024, masana'antar shirya fina-finan Nollywood ta shiga jimami na rashin fitaccen jaruminta mai suna Otunba Ayobami Olabiyi.
Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari ya yi magana kan rashin ƴarsa mai suna Fatima Kyari inda ya nuna alhinisa da yi mata addu'ar samun rahama a gobe kiyama.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar matar tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja mai suna Tinuade Ladoja a jiya Litinin 14 ga watan Oktoban 2024 a Ibadan.
Rahotannin da muka samu da safiyar Litinin ya nuna cewa wani bene mai hawa 2 ya ruguje a layin Amusu da ke jihar Legas, hukumar LASEMA ta ce abin ya zo da sauki.
Yan bindiga sun kashe dan takarar jam'iyyar APC na kansila, Adeyinka Adeleke a yankin Jide Jones da ke karamar hukumar Abeokuta ta Kudu a jihar Ogun.
Abun Bakin Ciki
Samu kari