Abun Bakin Ciki
Wata mummunar gobara da ta tashi ta ƙone shaguna 529 a kasuwar Shuwaki, a Kano, yayin da wani hatsarin tankar mai ya hallaka mutum 3 a Kura cikin kwana guda.
Hatsarin mota ya kashe mutane shida a titin Awka–Onitsha da ke jihar Anambra bayan karo tsakanin tipa da bas da ke dawowa daga jana’iza a jihar Ebonyi
Rahotanni sun nuna cewa wasu hatsabiban 'yan bindiga sun sace sace mai martaba Ojibara na Bayagan, watau Oba Kamilu Salami, a safiyar ranar Asabar din nan.
Gwamnan Delta da wasu manyan jiga-jigai a jihar Delta sun halarci jana'izar tsohon gwamna a lokacin mulkin sojoji, Paul Ufuoma Omu a wata coci yau Asabar.
An shiga fargaba a birnin Asaba da ke jihar Delta bayan gano gawar tsohuwar Alkalin Delta, Mai Shari'a, Ifeoma Okogwu, an daure ta an kuma lalata gidanta.
Kungiyar ANTP ta karyata jita-jitar cewa fitaccen jarumin Nollywood, Lere Paimo (Eda Onile Ola) ya rasu, tana tabbatar da cewa yana raye kuma lafiya kalau.
Wata kotun Rivers ta yanke wa ɗalibin jami'ar UNIPORT, Damian Okoligwe, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe masoyiyarsa Justina Otuene da sassara jikinta.
Ɗan sanda ya rasu bayan ‘yan daba sun soke shi a birnin Akure da ke jihar Ondo, inda ake zargin rikici ya barke yayin aikin sintiri da yake yi a yankin.
Wata mata ta rasa rayuwarta bayan ‘yan bindiga sun harbe ta yayin da take ɗaukar bidiyon harin da aka kai wa jerin gwanon motocin Chris Ngige a Anambra.
Abun Bakin Ciki
Samu kari