Abuja
Wasu kungiyoyin fararen hula da 'yan ƙasa masu kishin ƙasa sun bukaci a binciki tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari, kan kashe $1.5bn a matatar Port Harcourt a Rivers.
Bayan kisan kiyashin da aka yi wa Hausawa a Edo, dan majalisar tarayya, Kabiru Rurum, ya shawarci jama’arsa su daina farauta a Kudu saboda matsalolin tsaro.
Shugabannin SDP sun karbi tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Sanata Muhammad Ubali Shitu zuwa SDP. Nasir El-rufa'i da Hamza Al-Mustapha sun masa baya
Gwamnatin Bola Tinubu Najeriya za ta tura tawaga mai ƙarfi zuwa Jamhuriyar Nijar domin isar da sakon shugaban ga Janar Abdourahamane Tchiani a gobe Laraba.
Yayin da PDP ke kokarin ɗinke barakarta, shugaban ƙaramar hukumar birni a Abuja watau AMAC, Hon. Christopher Zakka Maikalangu ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Shugaban jam’iyyar APC ta Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar na ƙoƙarin samun ƙarin jihohi fiye da guda 21 da a yanzu take da su.
Bayan sace wata motar ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a masallacin Juma'a, Nuhu Ribadu, rundunar ‘yan sanda ta fara bincike kan lamarin.
Rahotanni sun bayyana yadda babban jigo a jam'iyyar APC, Rauf Adeniji ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane, bayan sace shi a watan Janairun shekarar 2025.
Hukumar NiMet ta bayyana cewa za a buga zafi mai mai tsanani a wasu jihohin Arewa 18. Yanayin zai hada da Kano, Gombe, Jigawa, Benue da birnin tarayya Abuja.
Abuja
Samu kari