Abuja
Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo, ya musanta tuhume-tuhume 12 da EFCC ta shigar masa kan zargin wanke kudade da daukar nauyin ta'addanci.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sanya bai da farin jini a wajen ma'aikata. Ya ce bai amincewa a kashe kudi a banza.
Babbar kotun Abuja ta amince da bukatar tsare tsohon shugaban CCT na kasa, Danladi Umar a gidan yari bayan gurfanar da shi kan zargin karbar rashawa.
Zaman Majalisar Wakilai ya rikice bayan bukatar gayyatar Shugaba Bola Tinubu domin ya yi bayani kan jinkirin aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025.
Binciken kwa-kwaf ya tabbatar da cewa bidiyon da ke nuna Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ministoci suna rera tsohuwar wakar kasa ba sabon bidiyo ba ne.
Mai ba Atiku Abubakar shawara kan yada labarai, Paul Ibe, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Femi Gbajabiamila kafin binciken ICPC ya fara.
Rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja ta kaddamar da samame a wurare masu haɗari. Ta kama sama da mutum 500 da ake zargi.a yankunan Abuja da kewaye.
Wata kungiyar farar hula da ke ayyukan siyasa ta CNPP ta fara kira a sauke manyan jami'an gwamnatin Bola Tinubu kan samar da ma'aikatar bogi a Najeriya.
Gwamnatin Tarayya ta raba takin zamani da sauran kayan noma ga manoma 5,642 a jihar Gombe domin tallafa musu a daminar 2026 da ƙara samar da abinci.
Abuja
Samu kari