Abuja
Majalisar Dattawa karkashin shugabancin Sanata Godswill Akpabio sun shiga ganawar sirri kuma ta gaggawa da ake zargin bai rasa nasa nasaba da ministocin Tinubu.
Dan takarar majalisar Tarayya a PDP a mazabar Kabba-Bunu Ijumu a jihar Kogi, Honarabul Olaiya Michael ya riga mu gidan gaskiya a jiya Laraba 19 ga watan Yuli.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya koka kan kwaranyowar 'yan ta'adda da wasu masu aikata miyagun laifuka zuwa jiharsa daga jihohin da ke makwabtaka da.
Majalisar Wakilan Najeriya ta tabbatar da nadin hafsoshin tsaro bayan Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika su ga majalisar don tantancewa a makon da ya gabata.
Awanni 48 bayan samun sauyin shugabanci a APC, Kwamitin NWC ya shirya zama da gwamnonin jam'iyya mai mulki kan muhimman abubuwan da suka faru a cikin gida.
Kungiyar Malaman Kwalejin Ilim a Najeriya ta umarci mambobinta da suke zuwa wurin aiki sau biyu a sati saboda halin da ake ciki a na cire tallafin man fetur.
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta dauki mummunan mataki a kan kungiyoyin 'yan kasuwa dake kara farashin kayayyaki da na masarufi babu gaira babu dalili a Najeriya.
Wani matashi da ya arce da wata mota ta naira miliyan 55 a kwanakin baya a Abuja, ya bayyana cewa ba da nufin sata ya dauki motar ba. Ya ce kawai dai ya tafi.
Wani magidanci a birnin tarayya Abuja, Raphael Chima, ya nemi Kotun kwastumare mai zama a birnin tarayya ra raba aurensa da Joy saboda bata kaunar zaman lafiya.
Abuja
Samu kari