Majalisar dokokin tarayya
Majasar dokokin jihar Kano ta ɗaukaka ƙara kan dokar masarauta wadda ta saukw sarakuna biyar da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya naɗa a lokacin mulkinsa.
'Yan Najeriya sun bayyana rashin jin dadinsu ga yadda aka fara tunanin siyan sabbin jirage ga shugaban kasa da mataimakinsa a cikin wannan yanayi.
Tsohon kakakin majalisar wakilar Yakuba Dogara ya bayyana babban kalubalen da tsarin mulkin farar hular ke fuskanta, wanda ya danganta da talauci.
Ɗan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Ifelodun/Boripe da Boluwaduro a jihar Osun, Soji Adetunji ya gwangwaje ƴan mazaɓarsa bayan harin da matasa suka kai masa.
Kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta sayo sababbin jiragen sama domin amfanin shugaban kasa da mataimakin sa.
Majalisar dattawa ta ce akwai kura-kurai a taken Najeriya da hukumar NOA ta ta gabatar da shi. Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya ba NOA umarni ta yi gyara.
Majalisar wakilan Najeriya ta dauki gabarar binciken musabbabin yawan matsala da jirgin kasan Abuja-Kaduna ke samu a kwanakin nan, kan haka aka gayyaci minista.
Wasu ƴan majalisar wakilan tarayya sun fara kiran a sauya tsarin mulkin Najeɗiya ya koma zango ɗaya ga shugaban ƙasa da kuma tsarin karba-karba a Najeriya.
Majalisar wakilan tarayya ta saurari kudurorin doka guda shida da za su takaita wa'adin shugaban kasa da gwamnoni da samar da ofishin mataimakin shugaban kasa 2.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari