Mafi karancin albashi
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa babu gwamnatin da za ta iya biyan ma'aikata N497000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba, ta ce abun ya yi yawa.
Gwamnatin jihar Edo karkashin jagorancin Gwamna Godwin Obaseki ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma'aikata a jihar mai arzikin man fetur.
Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta shawarci gamayyar kungiyoyin kwadago su daina mafarki. Kungiyar Kwadago ta NLC na neman N497,000 a matsayin mafi karancin albashi.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta fara biyan mafi ƙarancin albashin N30,000 ga ma'aikata a watan Yuni mai zuwa.
A fafutukar da Kungiyar kwadago ke yi na tilasta gwamnati biyan mafi karancin albashin da zai tabuka wani abu a rayuwar ma’aikata. Ta nemi N497,000.
Kungiyoyin kwadago sun rage bukatarsu a mafi ƙarancin albashi amma sun ce ba za su karɓi sabon tayin da gwamnatin tarayya ta gabatar na N57,000 ba.
Duk da gwamnati tarayya ta motsa, kungiyoyin kwadago sun nuna ba za su yarda da N54,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta gabatar da N54,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin da take son ta biya ma'aikata a Najeriya bayan an yi watsi da N48,000.
Yayin da kungiyoyin kwadago a Najeriya na ci gaba da fafutukar wasu jihohin kasar nan su biya N30,000 mafi karancin albashi ko su dauki matakin yajin aiki.
Mafi karancin albashi
Samu kari