Mafi karancin albashi
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sanya labule da shugabannin kungiyoyin kwadago a fadarsa da ke Aso Rock Villa. Za su tattauna kan mafi karancin albashi.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ka iya sanar da adadin da aka amince da shi a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata bayan ganawa da ƴan kwadago.
Kungiyar yan kwadago ta yi barazanar tafiya yajin aiki na tsawon kwana 30 idan majalisa ta yi doka marar kan gado kan karin albashin ma'aikata a fadin Najeriya.
Idan har aka zabe shi matsayin gwamnan Ondo, Ayodele Olorunfemi, dan takarar gwamna na LP ya ce zai biya N120,000 matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikata jihar.
Bayan tsawon lokaci ana tattaunawa da kace-nace kan batun sabon mafi ƙarancin albashi, watakila Bola Tinubu ya miƙa kudirin ga majalisar tarayya a makon gobe.
Gwamnatin tarayya ta bayyana yaƙinin cewa daga nan zuwa mako mai zuwa za a kawo karshen ja-in-ja kan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya nemi 'yan kwadago su amince a biya N62,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi. Sai dai ma'aikatan sun dage kan N250,000.
'Yan kwadago sun yi magana bayan sun gana da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Sun dage cewa sai an biya N250,000 matsayin mafi karancin albashi.
Yayin da kungiyoyin ƙwadago su ka dage cewa lallai sai gwamnatin tarayya ta yi ƙari mai gwaɓi kan albashin ma'aikata, shugaban zai gana da kungiyoyi.
Mafi karancin albashi
Samu kari