Gwamnatin Amurka ta dakatar da neman katin zama a kasar da na katin zama dan kasa ga 'yan Najeriya. An dauki matakin ne bayan umarnin shugaba Donald Trump.
Gwamnatin Amurka ta dakatar da neman katin zama a kasar da na katin zama dan kasa ga 'yan Najeriya. An dauki matakin ne bayan umarnin shugaba Donald Trump.
Tsofaffin yan majalisar tarayya daga Kano sun amince Bola Ahmed Tinubu ya yi shekara takwas a mulki, sun giyi bayan Sanata Barau ya zama gwamnan Kano.
Kungiyoyi da dama da masu ruwa da tsaki sun yi kira ga wasu manyan 'yan siyasa kan ka da su fito takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Tsohon Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Sanata Agboola Ayoola ya mika wasikar ficewarsa daga jam'iyyar PDP a jihar Oyo, ya ce zai canza akalar siyasa.
Mai taimakawa tsohon gwamnan Benue, Gabriel Suswam, ya karyata jita-jitar cewa ya koma APC, yana cewa gayyatar Gwamna Alia ba ta da nasaba da siyasa.
Jam'iyyar APC ta hana yan siyasa biyu shiga zaben fidda gwanin da zata shirya domin tsaida dan takarar gwamnan jihar Ekiti a zaben da za a yi a shekarar 2026.
'Dan takarar ADC a Anambra, John Nwosu, ya rantse a kotu cewa zai yi wa’adi ɗaya kacal idan ya ci zabe, domin jaddada shugabanci na gaskiya da adalci ga shiyyoyi.
Yayin da ake shirye-shiryen zaben shekarar 2027, Fasto Boris Jedidiah daga kasar Kamaru ya ce Bola Tinubu zai sake lashe zaben shugaban ƙasa a 2027.
Kwamitin rikon kwarya da APC ta kafa a jihar Enugu ya tabbatar da cewa Gwamna Peter Mbah da mukarrabansa za su dawo jam'iyya mai mulkin Najeriya a makon gobe.
Wani daga cikin masoyan Abdullahi Ganduje, Malam Umar Idris Shuaibu, ya ce Arewa, musamman Kano, za ta mara wa Tinubu baya a zaben 2027 saboda ayyukan alheri.
Tsohon minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya gana da shugaban jam'iyyar PDP mai adawa, Ambasada Umar Iliya Damagum tare da tawagarsa a Abuja.
Siyasa
Samu kari