Bayan Sauya Shekar Kwankwaso, An Samu Gwamna na Farko da Zai Koma Jam'iyyar ADC
Bauchi, Nigeria - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya tabbatar da cewa ADC ce zabinsa a matsayin jam'iyyar diyasar da zai koma bayan ya bar jam'iyyar PDP.
Hakan na nuna cewa lamarin da yiwuwar Gwamna Bala ya fice daga jam’iyyar PDP da ke fama da rikice-rikice, yayin da yan adawa ke shirin kulla hadaka mai karfi gabanin zaben 2027.

Source: Twitter
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a Bauchi ranar Talata, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Jim kadan bayan wata ganawar sirri da tawagar ADC karkashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, Gwamna Bala ya ce ADC ce zabinsa na gaba.
Ya ce bayan tattaunawa da shawarwari da dama, ADC ta zama jam’iyyar da ta fi dacewa da shi da abokan siyasarsa.
“Mun bar dukkan kofofinmu a bude, har da APC, amma mun gano cewa ba za mu zauna a inda ba a son mu ba. Dole ne mu nemo mafita a cikin bangaren adawa,” in ji Bala Mohammed.
Ya bayyana ADC a matsayin jam’iyya mai dorewa kuma mafi karbuwa ga masu ruwa da tsaki da yake tuntuba, yana mai cewa ya yi jinkirin yanke hukunci na karshe ne saboda tattaunawa da yake yi da bangarorin siyasa daban-daban.
A cewarsa:
“Saboda ina kula da muhimman bangarori biyu, Bauchi da kasa baki dayadole ne mu yi komai yadda ya kamata. Dole ne mu hada kan muradun jam’iyya a matakin kasa da jiha, musamman a cikin PDP, hakan ya sa tattaunawa ta dauki lokaci.”
Gwamna Bala ya kuma bayyana cewa yunkurin shiga APC a baya bai yi nasara ba, duk da ganawar da ya yi da Shugaban Kasa Bola Tinubu da shugabannin jam’iyyar na kasa
Ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tuntubar muhimman masu ruwa da tsaki domin kauce wa kura-kurai, yana mai jaddada muhimmancin hadin kai wajen gina bangaren adawa mai karfi.
“Mutanen ADC ‘yan uwanmu ne. Wasu sun shiga tun da wuri, mu kuma yanzu muke shirin shiga,” in ji shi.
Asali: Legit.ng
