Yadda ake bikin shigar Kwankwaso cikin jam’iyyar ADC a Kano

All posts
Key Events
Analysis
Exclusive
9 Posts
Sort by
Aisha Ahmad avatar
daga Aisha Ahmad

Ɗan Kwankwaso ya bar NNPP, zai bi ubansa zuwa ADC

Mustapha Rabiu Kwankwaso, ɗan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP, inda ya nuna shirin komawa ADC.

Mustapha Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin, inda ya ce bar NNPP bayan ya yi nazari mai zurfi.

Ya ce:

“Ina sanar da al’umma cewa daga yau na fice daga jam’iyyar NNPP.”

Ya ƙara da cewa a halin yanzu yana kan hanyar kammala shigar sa cikin jam’iyyar ADC, yana mai nuna kwarin gwiwa kan sabon matakin da zai ɗauka a harkokin siyasa.

A cewarsa, shawarar da ya yanke na komawa ADC ta samo asali ne daga imanin da yake da shi cewa jam’iyyar na da kyakkyawar dama wajen kawo sauyi mai ma’ana a Najeriya, musamman a jihar Kano.

Mustapha ya bayyana cewa hangen nesa da manufofin jam’iyyar ADC suna ba da ingantaccen dandali wajen tabbatar da shugabanci nagari, bunƙasa tattalin arziki da kuma inganta rayuwar al’umma.

Mustapha Kwankwaso, wanda ke rike da mukamin sakataren ƙungiyar Kwankwasiyya, ya jaddada aniyarsa ta yin aiki tare da masu ruwa da tsaki masu ra’ayi iri ɗaya domin cimma muradun ci gaba na bai ɗaya.

Aisha Ahmad avatar
daga Aisha Ahmad

Kwankwaso ya koma ADC da dukkanin magoya bayansa

Tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa a NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ya sauya sheka zuwa ADC.

BBC Hausa ta wallafa cewa ya bayyana haka ne a wani taro da ke gudana a yau Litinin 30 ga watan Maris, 2026 a gidansa da ke Miller road a Kano.

A taron da jiga-jigan ADC da dubbunnan masoyansa suka halarta, Kwankwaso ya ce ya sauya sheƙa tare da baki ɗaya magoya bayansa.

Aisha Ahmad avatar
daga Aisha Ahmad

Dubunnan mutane sun yi dandazo a gidan Kwankwaso

Dubunnan magoya baya sun yi dandazo a Miller road inda a yanzu haka ake bikin sauya shekar Sanata Rabi'u Musa kwankwaso.

Hotunan da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a shafin Facebook sun nuna yadda mutane suka yi dafifi yayin da Kwankwaso ya ke masu maraba.

Aisha Ahmad avatar
daga Aisha Ahmad

Kwankwaso ya tarbi Peter Obi

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, a Kano domin halartar bikin sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar ADC.

A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ADC ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ziyarar ta Obi na da nasaba da goyon bayan sabon matsayi da Kwankwaso ya ɗauka a siyasar ƙasar nan.

Da karfe 1:41 na ranar yau sanarwa ta gabata cewa Peter Obi ya iso Kano inda ake Kwankwaso zai zama ‘dan jam’iyyarsu ta ADC.

Kafin nan, bayani ya gabata daga wani shafin masoyan Peter Obi cewa yana kan hanyar zuwa babban taron da za a yi a garin Kano.

Muhammad Malumfashi avatar Aisha Ahmad avatar
daga Muhammad Malumfashi and Aisha Ahmad

Kwankwasiyya ta yi manyan baki

Legit Hausa ta fahimci manyan ADC na kasa irinsu

1. Aminu Waziri Tambuwal

2. John Oyegun

3. Emeke Ihedioha

4. Rotimi Amaechi

5. Rauf Aregbesola

6. Lawal Daura

duk suna gidan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso

Muhammad Malumfashi avatar Aisha Ahmad avatar
daga Muhammad Malumfashi and Aisha Ahmad

Shugaban ADC yana Kano

Bayanan da aka samu daga shafin hadimin Kwankwaso sun tabbatar da isowar David Mark gidan tsohon jagoran na jam'iyyar NNPP.

David Mark shi ne shugaban ADC na kasa baki daya wanda sakatarensa watau Rauf Aregbesola ya yi zama da Kwankwaso kafin yanzu.

Muhammad Malumfashi avatar Aisha Ahmad avatar
daga Muhammad Malumfashi and Aisha Ahmad

Hallarar wasu manyan ‘yan adawan Arewa

Da kusan karfe 12:30 Saifullahi Hassan ya wallafa hotunan tsohon ‘dan takarar gwamnan Jigawa, Aminu Ringim a Miller Road.

Bayan nan an ga tsohon ‘dan majalisar tarayya a Katsina, Ahmad Babba Kaita wanda babban jigo ne a jam’iyyar ADC a Katsina.

An ga hoton Ahmad Babba Kaita da jar hula a kafar Facebook.

Aisha Ahmad avatar
daga Aisha Ahmad

Kabiru Marafa ya isa gidan Kwankwaso

Karfe 11:27 aka ga hotunan Rabiu Kwankwaso tare da Sanata Kabiru Garba Marafa wanda suka yi aiki tare da shi a majalisar dattawa.

Lokacin da Kwankwaso ya fito a yau, tsohon 'dan majalisar na Zamfara ta tsakiya yana cikin wadanda suka fara haduwa da shi.

Muhammad Malumfashi avatar Aisha Ahmad avatar
daga Muhammad Malumfashi and Aisha Ahmad

Taron Caucus a gidan Kwankwaso

A safiyar Litinin aka ji labari cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana jagorantar taron Kwankwasiyya a garin Kano.

An yi taron Caucus ne a gidan Madugun na darikar Kwankwasiyya da ke Miller Road a Kano.

Cikin mahalarta wannan taro akwai manyan tafiyar ta jar hula irinsu Sanata Rufai Sani Hanga da Dr. Yusuf Kofarmata wanda shi ne sakatare.

Hadimin babban ‘dan siyasar Saifullahi Hassan, ya wallafa bidiyon wannan taro a Shafin Facebook da kimanin karfe 10:00 na safe.

Mai taimaka wa ‘dan siyasar ya rubuta:

“Mai Girma Jagora Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci zama na musamman tareda masu ruwa da tsaki wato Caucus kan shirye-shiryen shiga jam’iyyar ADC da zaiyi a wannan rana ta Litinin”