Dubun Wasu Shugabannin PDP Ta Fara Cika, Damagum Ya Yi Tone Tone a Taron BoT

Dubun Wasu Shugabannin PDP Ta Fara Cika, Damagum Ya Yi Tone Tone a Taron BoT

  • Damagum ya zargi wasu daga cikin shugabannin PDP, ciki har da mambobin BoT, da hannu rikicin da ke faruwa a kwamitin gudanarwa (NWC)
  • Muƙaddashin shugaban PDP ya gargadi shugabanni da su guji daukar matakan da ka iya kawo cikas ga zabukan shugabanni na yankuna da ke tafe
  • Ya ja kunne cewa haddasa rikici domin cimma burin siyasa na kashin kai ba zai amfani jam’iyyar ba, domin hakan zai iya lalata damar cimma nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Mukaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya zargi wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar, ciki har da mambobin kwamitin amintattu (BoT), da hannu a rikicin da ke faruwa.

Damagum ya gargadi sauran shugabannin PDP a kowane mataki da su guji duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zabukan shugabanni na yankuna da ke tafe.

Kara karanta wannan

Yaki da talauci: Gwamnan Jigawa ya raba tallafin kudi ta katin ATM

Taron BoT.
Damagum ya bayyana masu hannu a rigingimun cikin gida da suka addabi PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne a jawabin bude taron kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP karo na 78 da aka gudanar a Abuja, rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban PDP ya faɗi masu rura wutar rikici

Damagum ya ce:

"Bari na faɗi wani abu da ya rataya a wuyana, wasu daga cikin shugabannin PDP ke rura wutar rikicin da ake gani yau a kwamitin gudanarwa (NWC) maimakon su haɗa kanmu."
"Kuma a matsayinmu na ƴan jam'iyya masu sanin ya kamata, wasu daga cikinmu murɗaɗɗu ne, ya kamata mu kalli kanmu, mu binciki kanmu, jam'iyyar nan ta PDP tana da muhimmanci.
"PDP tamu ce ita gare mu, abin takaici ne abubuwan da ke faruwa. Zan faɗi gaskiya mun san aikin NWC, wasu a nan mambobin NWC ne, ina matsayin shugaba sai naga ana kiran mambobi ne su je wurin wasu."

Damagum ya gargaɗi jiga-jigan PDP

Damagum ya gargaɗi masu ruwa da tsaki a PDP da su gujewa rura wutar rikicin da jam'iyyar ke fama da shi saboda wasu burikansu na kashin kai.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

A rahoton Tribune, shugaban PDP ya ƙara da cewa:

"Ina amfani da wannan dama domin na gargade mu, na gargadi shugabanninmu, kuna da buri, amma ba za ku hau doki matacce domin isa inda kuke so ba.
"Idan kuna haddasa rikici ne kawai domin cimma burin kanku, watakila ku samu abin da kuke so, amma burinku ba zai cika ba, domin a lokacin, kun jikkata dokin da kuke son hawa don isa ga burinku.

Damagum ya bayyana cewa, duk da kalubalen da jam’iyyar ke fuskanta, ita ce kadai fatan da ‘yan Najeriya ke da shi.

Jami'an tsaro sun kai ɗauki hedkwatar PDP

A wani labarin, kun ji cewa jami'an tsaro sun mamaye hedkwatar PDP ta ƙasa bayan rigima ta kaure a wurin taron Majalisar amintatti watau BoT.

Rigimar ta ɓarke ne lokacin da manyan kusoshin PDP biyu da ke rigima kan kujerar sakatare suka isa wurin, lamarin da ya kai da marin Ude-Okeye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel