A karshe, Jonathan Ya Samu Damar Gwabzawa da Tinubu a 2027

A karshe, Jonathan Ya Samu Damar Gwabzawa da Tinubu a 2027

  • Jam’iyyar PDP ta bukaci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027 a karkashinta
  • PDP ta bayyana cewa yana da muhimmanci shugaba Jonathan ya ci gaba da ayyukan da ya fara a lokacin mulkinsa
  • Jam’iyyar ta gargade shi kan sukar da APC ta masa a baya, tana mai cewa ya zama mai hangen nesa kan yabonsa da ta fara a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta fito karara ta bukaci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027.

Mataimakin sakataren yada labaran PDP na kasa, Ibrahim Abdullahi ya bayyana cewa jam’iyyar na da matukar kaunar ganin Jonathan ya sake komawa mulki.

Bola Tinubu
PDP ta bukaci Jonathan ya yi takara a 2027. Hoto: Goodluck Ebele Jonthan|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A wata hira da ya yi da jaridar Punch, Abdullahi ya ce PDP ita ta gina tushe da matakin siyasar Jonathan, don haka bai dace ya yi takara da wata jam’iyya ba

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 6 da gwamnatin Tinubu za ta yi wa 'yan Najeriya a shekarar 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa PDP tana alfahari da irin manyan mutane da ta samar wa Najeriya, ciki har da ministoci da manyan shugabanni a kasashen duniya.

2027: Jonathan zai gwabza da Tinubu

Mataimakin sakataren yada labaran PDP, Ibrahim Abdullahi ya ce jam’iyyar PDP ta dade tana jiran tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sake fitowa takara a karkashinta.

“Mun yi imani Jonathan zai iya ci gaba da ayyukan da ya fara karkashin PDP. Jam’iyyar tana da tarihi mai kyau na samar da shugabannin da suka fitar da Najeriya kunya,”

- Ibrahim Abdullahi

Ya kuma yi tsokaci kan irin sukar da APC ta yi wa tsohon shugaban kasar a baya, yana mai cewa idan Jonathan ya tsaya takara da APC, hakan zai bayyana rashin gaskiyar jam’iyyar.

APC ta yi martani kan takarar Jonathan

Darakta Janar na yada labaran APC, Bala Ibrahim, ya ce jam’iyyarsu ba za ta ji tsoro ba idan Jonathan ya tsaya takara karkashin APC ko wata jam’iyya.

Kara karanta wannan

Jagoran PDP ya fadi wanda ake amfani da shi domin rusa jam'iyyar adawa

“Mun kayar da Jonathan a lokacin da yake kan mulki. Idan ya tsaya takara yanzu, hakan ba zai zama wani kalubale ba,”

- Bala Ibrahim

Ya kara da cewa ko irin Jonathan 10 ake ajiye takara ba za su iya kayar da Bola Tinubu ba a zaben 2027.

An soki Atiku kan takarar 2027

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo ta nuna damuwa kan kalaman Atiku Abubakar a kan 2027.

Kungiyar ta ce abin takaici ne yadda Atiku ke goyon bayan takarar dan Arewa 2027 wanda hakan ke nuna rashin damuwarsa ga Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng