Kotu Ta yi Hukunci kan Karar da PDP Ta Shigar da APC bayan Zaben Gwamnan Ondo
- Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya yabawa kotu kan korar karar da aka shigar da shi a kan cancantarsa a zaben gwamna
- Kotun ta kori karar da ɗan takarar PDP, Agboola Ajayi ya shigar, inda ta bayyana cewa ba ya da hurumin shigar da ƙarar
- Mai shari’a Toyin Bolaji Adegoke ta bayyana cewa karar ta wuce kwanaki 14 da dokar zabe ta tanada domin shigar da korafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum
Jihar Ondo - Rikicin siyasar Ondo ya dauki sabon salo bayan kotun tarayya ta kori karar da ɗan takarar PDP, Agboola Ajayi ya shigar kan cancantar gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Karar, wacce aka gabatar gaban Mai shari’a Toyin Bolaji Adegoke na kalubalantar cancantar gwamnan da mataimakinsa, Olayide Adelami a zaben gwamna na 16 ga Nuwamba.
Legit Hausa ta gano yadda shari'ar ta gudana ne a cikin wani sako da hadimin gwamnan Ondo, Ebenezer Adeniyan ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaben Ondo: Kotun ta kori karar PDP
Vanguard ta wallafa cewa mai shari’a Adegoke ta ce PDP da ɗan takararta ba su da hurumin shigar da ƙarar tare da cewa an shigar da ita bayan wa’adin kwanaki 14 da doka ta kayyade.
A karkashin haka, kotun ta kori karar da PDP ta shigar gaban alkalin domin neman a soke sahihancin shigar 'yan takarar APC zaben.
Dalilan da lauyoyin gwamna suka gabatar
Lauyoyin gwamna da mataimakinsa sun yi nasarar kare sahihancin takardun sunayen mataimakin gwamna, Adelami.
Lauyoyin sun ce WAEC ta tabbatar da sunan “Adelami Owolabi Jackson” a 1974 yayin da jami’ar Ambrose Alli ta tabbatar da digirin da ta ba shi da sunan “Adelami Olaide Owolabi” a 1982.
Sun bayyana cewa canjin tsari ko rubutun sunaye ba ya rushe ingancin takardu kuma hakan ba zai sa PDP ta kalubalanci takararsa ba.
Gwamna Aiyedatiwa ya yaba da hukuncin kotu
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya bayyana gamsuwarsa da hukuncin kotun, yana mai cewa hakan zai ba shi damar ci gaba da jagorancin jihar ba tare da wata tangarda ba.
A yanzu haka dai kallo zai koma kan jam'iyyar PDP domin ganin matakin da za ta dauka bayan hukuncin kotun.
An ki karbar 'yan PDP a Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa wasu yan jam'iyyar PDP sun ga ta kansu yayin aka ki karbarsu a APC bayan sun sauya sheka a jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a gundumar Ogbagi da ke Akoko inda shugabannin jam'iyyar suka ce ba za su amince da su ba a cikin tafiyar APC.
Asali: Legit.ng