Zaɓen Edo Ya Ɗauki Zafi, Ɗan Takarar Gwamna Ya Koka kan Bayanan da Ake Turo Masa
- Ɗan takarar gwamna a inuwar Labour Party, Olumide Akpata ya bayyana cewa suna samun labarai marasa daɗi game da zaben da ke gudana
- Akpata ya ce duk da shi ba mutum ba ne me ɗaukar maganganu, amma zai gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar abin da aka faɗa masa
- Wannan dai na zuwa ne yayin da zaɓe ya kankama a jihar Edo yau Asabar, 21 ga watan Satumba, 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo - Ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar LP a zaben jihar Edo da ke gudana, Olumide Akpata ya bayyana danuwarsa kan wasu abubuwan da ke faruwa.
Mista Akpata ya ce akwai damuwa sosoai a bayanan da yake samu kan yadda zaɓe ke tafiya a lungo da sako na jihar Edo yau Asabar, 21 ga watan Satumba, 2024.
A ruwayar TVC, ɗan takarar LP ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Muna samun bayanai mara daɗi daga sassan jihar nan amma ni da mutum ba ne da zai fito ya kama surutu ɓa tare da yin bincike ba, za mu ci gaba da sa ido kan zaɓen.
Edo 2024: Akpata ya kada kuri'arsa
Akpata ya kada kuri'arsa a gudumar Oredo 6, Unit 11, inda aka ga yana murmushi tare da ɗaga wa magoya bayansa hannu.
Da yake jawabi bayan kaɗa kuri'arsa, ɗan takara LP ya bayyana cewa zaben na gudana lami lafiya ba tare da tangarda ba.
Olumide Akpata ya ƙara da cewa yana fatan duk wani ɗan jihar Edo zai ƙaɗa kuri'arsa cikin sauƙi ba tare da matsala ba kamar yadda ya yi, Channels tv ta kawo.
Kapata ya bayyana kwarin guiwar samun nasara a zaɓen, yana mai cewa idan har aka tafi da zaɓen cikin adalci har karshe, kowa zai yi na'am da sakamakon.
Gwamna Obaseki ya gamsu da zaben Edo
A wani rahoton kuma Gwamna Obaseki ya isa rumfar zaɓensa da ke makarantar firamare ta Emokpae a Benin, babban birnin jihar Edo kuma ya kaɗa kuri'arsa.
Godwim Obaseki na jam'iyyar PDP ya bayyana gamsuwa da yadda zaɓen ke gudana tare da fatan hakan ya ɗore har lokacin tattara sakamako.
Asali: Legit.ng