"Ni Bawan Talakawa Ne," Gwamna Ya Soki Wasu Manya bayan Ganawa da Tinubu
- Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya ce al'umma ne suka zaɓe shi kuma su zai yi wa aiki ba wasu tsirarun mutane ba
- Gwamna Alia ya bayyana haka ne da yake hira da ƴan jarida a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja bayan ganawa da Bola Tinubu
- Ya ce gwamnatinsa ta maida hankali wajen tallafawa mutane musamaman matasa domin gina masu gobe mai kyau a Benuwai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue - Gwamna Hyacinth Alia na Benuwai ya ce gwamnatinsa ta maida hankali wajen samar da shugabanci na gari ga al’umma ba wai gina wasu tsirarun mutane ba.
Gwamna Alia ya ce al'umma ce a gabansa kuma su yake yi wa aiki ba wasu tsirararun mutane da ke kallon kansu a matsayin wasu manya ba.
Gwamnan Benuwai ya gana da Bola Tinubu
Ya faɗi haka ne yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja, Channels tv ta ruwaito hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce ya je fadar shugaban ƙasa ne domin yi wa shugaba Tinubu bayani kan al’amuran jihar Binuwai, musamman matsalar tsaro.
Gwamna Alia ya faɗi abin da ke gabansa
A cewar Gwamna Alia, talakawansa ne suka zabe shi domin ya yi musu hidima kuma sune a gabansa ba wai masu daukar kansu a matsayin masu ƙarfin iko a jihar Benuwai ba.
"Mutane na zo na yi wa aiki, ban san su waye manya ba, al'umma ta kawo ni kan wannan kujera shiyasa duk abin da ya shafe su nake ɗaukarsa da gaske, idan shugaba ya zama bawan talakawansa komai na tafiya daidai."
"Na san zafin da suke ji amma abin ya fi kamata shi ne su ɗauki lamarin da sauki su sauƙaƙawa kansu da kuma talakawa," in ji Alia.
Gwamma ya fara ba matasa tallafi
Gwamnan ya kuma bayyana cewa a yanzu gwamnatinsa na maida hankali ne wajen ba al’ummar jihar Binuwai, musamman matasa tallafi, Daily Post ta rahoto.
Ya ce sama da matasa 10,000 ne ake horas da su sana’o’in zamani yanzu haka kuma gwamnatin Benuwai ta ɗauki nauyin matasa zuwa kasar Sin domin koyon sana’o’i.
Tsagin APC a Benue ya soki Gwamna Alia
A wani rahoton kuma jam'iyyar APC ta caccaki Gwamna Alia Hyacinth na Benue kan rikicin siyasar cikin gidan a jihar da ke faruwa
'Ya 'yan jam'iyyar APC a Majalisar Tarayya su suka zargi gwamnan da neman ruguza jam'iyyar domin biyan buƙatar kansa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng