Katsina: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yanke Hukuncin Ƙarshe Kan Kujarar Ɗan Majalisar Tarayya
- Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta kawo karshen taƙaddama kan kujerar ɗan majalisar Faskari, Kankara da Sabuwa
- Kwamitin alkalan kotun ya tabbatar da Hon Shehu Ɗalhatu Tafoki a matsayin sahihin wanda ya lashen zaben da aka yi a 2023
- Tafoki, tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Katsina ya sha fama da shari'a tun bayan zaɓen fidda gwani a APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da Shehu Dalhatu Tafoki a matsayin halastaccen ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Faskari/Kankara/Sabuwa a Katsina.
Kotun ta sanar da haka ne yayin yanke hukunci kan ƙarar da ɗan takarar PDP, Jamilu Mohammed ya shigar gabanta ya na kalubalantar nasarar Tafoki.
Kotun daukaka kara mai zama a Abuja ta amince da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke tun farko, wanda ya tabbatar da nasarar Tafoki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton Leadership ya kawo cewa dukkan alƙalai uku da suka saurari shari'ar sun gamsu cewa babu wani kuskure a hukuncin da kotun zaɓe ta yanke.
Yadda Tafoki ya yi fama da shari'a
Hukuncin ya raba gardama kan taƙaddamar da ta shafe watanni 27 ana yi game da kujerar ɗan majalisar Faskari/Kankara/Sabuwa a jihar Katsina.
Tafoki ya fara fuskantar ƙalubale ne tun daga zaɓen fidda gwani na PDP, inda abokin karawarsa, Murtala Isah Kankara ya maka shi a kotu, rahoton Daily Trust.
Sai dai daga ƙarshe kotun ƙoli ta warware rigimar a lokacin da ta tabbatar da Shehu Ɗanhatu Tafoki a matsayin sahihin ɗan takarar APC.
A halin yanzu dai bayan shafe dogon lokaci yana fuskantar shari'a a kotu, Shehu Ɗalhatu Tafoki ya zama halastaccen ɗan majalisar Kankara, Faskari da Sabuwa.
Hon Tafoki ya yabawa Dikko Raɗɗa
Bayan yanke hukuncin karshe na kotun ɗaukaka ƙara, Hon. Tafoki ya godewa Allah tare da godewa gwamnan Katsina Mallam Dikko Umaru Radda bisa irin goyon bayan da ya ba shi.
Ya sha aƙwashin maida hankali kan ayyukasa na majalisa kuma ya ba da tabbacin cewa zai yi kokarin zuba ayyuka fiye da waɗanda ya yi a matsayin mataimakin kakakin majalisar Katsina.
2027: Ayodele ya ba ƴan adawa shawara
A wani rahoton Primate Elijah Ayodele ya bayyana dabarun da ya kamata ƴan adawa su yi idan suna son kayar da jam'iyya mai mulki a babban zaɓe na gaba.
Fitaccen limamin cocin ya faɗi dabarun ne a lokacin da ƴan siyasa suka fara shirye-shiryen zaɓen 2027 a Najeriya.
Asali: Legit.ng