Tsohon Kakakin Jam'iyyar APC Ya Tarewa Atiku Abubakar Faɗa kan Takara a 2027

Tsohon Kakakin Jam'iyyar APC Ya Tarewa Atiku Abubakar Faɗa kan Takara a 2027

  • Tsohon mataimakin kakakin APC ta ƙasa, Timi Frank ya shiga faɗan Alhaji Atiku Abubakar da Bode George a PDP
  • Timi Frank ya caccaki kalaman da Bode George ya yi kan takarar Atiku a 2027, ya ce Allah kaɗai ya san abin da zai faru
  • Jigon APC ya bayyana cewa bai kamata a ji bakin tsohon mataimakin shugaban PDP George a a fagen siyasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon mataimakin kakakin jam'iyyar APC ta ƙasa, Timi Frank ya tsoma baki kan surutun da ake yi game da yiwuwar takarar Atiku Abubakar a zaɓen 2027.

Timi Frank ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban PDP, George ba shi da ikon da zai yanke makomar siyasar Atiku a babban zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Malami ya bayyana hanya 1 da za a iya kayar da Shugaba Tinubu a zaɓen 2027

Timi Frank.
Tsohon mataimakin kakakin APC, Timi Frank ya soki kalaman Bode George kan Atiku Hoto: Timi Frank
Asali: Facebook

Timi Frank ya tarewa Atiku faɗa

Mista Frank ya yi wannan furuci ne a wata sanarwa da fitar ranar Alhamis domin maida martani ga kalaman Bode George, The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko dai Bode George ya buƙaci Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya jira 2031 idan yana son tsayawa takara domin mulki ba zai dawo Arewa ba a 2027.

Da yake maida martani, tsohon mataimakin kakakin jam’iyyar APC ya ce George bai ma cancanci yin magana kan irin wadannan batutuwa ba.

Tsohon kakakin APC ya soki George

"Taya mutumin da ke rayuwa bisa alfarmar kotun ƙoli zai shiga gonar Allah? Idan ba ku manta a 2009 babban kotun jihar Legas ta kama George da wasu mutum 23 da laifin zamba da almundahana.
"Kotun ƙoli ce ta wanke shi a 2013, ta yaya mutum kamarsa zai fito ya nuna ya san abin da zai faru nan gaba? A tunani na George bai cancanci tsoma baki a irin wannan batun ba."

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kalu ya bayyana mutum 1 da zai iya kwace mulki daga hannun Tinubu

- Timi Frank.

Mista Frank ya ƙara da cewa Allah ne kaɗai zai yanke makomar siyasar tsohon mataiamkin shugaban kasa Atiku Abubakar ba wani ɗan adam ba, a rahoton Punch.

APC ta magantu kan ficewar Moghalu

A wani labarin kun ji cewa APC ta bayyana cewa ko kaɗan ba ta ji mamaki ba da George Moghalu ya ɗauki matakin barin jam'iyyar bayan tsawon lokaci ba

Moghalu na ɗaya daga cikin iyayen APC da suka haɗu suka kafa ta, sai dai ya sanar da ficewa daga jam'iyyar saboda wasu dalilai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262