Magana Ta Ƙare, Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukunci kan Sahihancin Zaɓen Gwamnan APC
- Kotun ƙoli ta yanke hukuncin karshe a shari'ar zaben gwamnan jihar Imo da aka yi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023
- A zaman ranar Jumu'a, 23 ga watan Nuwamba, 2024 kotun ta kori karar PDP da LP, ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara
- Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta ayyana Hope Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan kammala tattara sakamako
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Imo - Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Hope Uzodinma karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Imo da ke Kudu maso Gabas.
Kwamitin alƙalai biyar na kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ne ya yanke wannan hukuncin ranar Jumu'a, 23 ga watan Agusta, 2024.
Kotun ta kori karar da jam'iyyar Labour Party (LP) da dan takararta, Athan Achonu suka daukaka zuwa gabanta saboda rashin cancanta, rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zaben Imo: Kotun koli ta yanke hukuncin ƙarshe
Shugaban kwamitin alkalan, Mai Shari'a Mohammed Baba Idris shi ne ya karanto hukuncin wanda ya kawo karshen duk wata taƙaddama kan nasarar Uzodinma.
Mai shari'a Mohammed ya warware dukkan ƙorafe-ƙorafe uku da masu kara suka shigar gaban kotun.
Alkalin ya bayyana cewa kotun koli ta fahimci cewa masu kara, jam'iyyar LP da ɗan takararta na gwamna, sun gaza gabatar da gamsassun hujjoji tun a kotun zaɓe.
Idan baku manta ba kotun zaɓe ta kori ƙarar LP da Athan Achonu bisa rashin cancanta, wanda kotun ɗaukaka ƙara kuma ta tabbatar da hakan
Daga nan sai Alkalin kotun kolin ya tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, wacce ta amince da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaɓe.
PDP da Anyanwu sun yi rashin nasara
Haka nan kuma kotun wacce ake yi wa taken daga ke sai Allah ya isa ta kori ƙarar jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Samuel Anyanwu, Channels tv ta ruwaito.
Gwamna Uzodinma ya samu kuri'u 540,308 wanda ya ba shi damar doke Sanata Anyanwu na PDP mai ƙuri'u 71,503 da Achonu na LP wanda ya tashi da kuri'u 64,081.
Kotu ta yanke hukunci a shari'ar zaben Bayelsa
Ku na da labarin kotun ƙoli ta kori ƙarar tsohon ƙaramin ministan fetur, Timipre Sylva kana ta tabbatar da nasarar Douye Diri a zaɓen Bayelsa.
A zaman yanke hukunci ranar Jumu'a, 23 ga watan Agusta, kwamitin alkalai biyar na kotun ya kori karar Sylva bisa rashin cancanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng