An Rantsar da Ododo Matsayin Sabon Gwamnan Jihar Kogi, Wa’adin Yahaya Bello Ya Kare

An Rantsar da Ododo Matsayin Sabon Gwamnan Jihar Kogi, Wa’adin Yahaya Bello Ya Kare

Jihar Kogi - A halin yanzu, Gwamna Usman Ahmed Ododo ya karbi ragamar mulkin jihar Kogi, bayan da wa'adin mulkin Yahaya Bello ya kare.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ana kan gudanar da bukin rantsar da sabon gwamnan a babban filin wasa na Muhammadu Buhari da ke Lokaja, inda Bello ya mika mulki ga Ododo.

Rahotanni sun bayyana cewa dubunnan 'yan jihar ne suka yi tururuwa a filin don gane wa idonsu yadda aka yi bukin rantsuwar, Daily Trust ta ruwaito.

Karashen labarin na zuwa...

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.