INEC Ta Sanar da Ranar Gudanar da Zabukan Cike Gurbi a Fadin Kasar Nan
- Biyo bayan samun kujerun ƴan majalisar tarayya da na jihohi da ba kowa, hukumar zaɓe ta ƙasa ta yi tsokaci kan yiwuwar gudanar da zaɓukan cike gurbi
- A wani taro na baya-bayan nan, shugaban INEC Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa, an zaɓi ranar Alhamis 1 ga watan Fabrairun 2024 don yin zaɓukan
- Ya bayyana cewa za a gudanar da zaɓen a mazaɓu 34 na tarayya da na jihohi waɗanda babu kowa a kujerunsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na shirin shirya zaɓukan cike gurbi a faɗin ƙasar nan a ranar Alhamis, 1 ga watan Fabrairun 2023.
Hukumar za ta shirya zaɓukan ne domin cike gurbin kujerun da suke a majalisun dokoki da na tarayya a faɗin ƙasar nan.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a wani taro da shugabannin jam’iyyun siyasa da aka kira domin fara shiri kan zaɓen mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A mazaɓu nawa za a gudanar da zaɓukan?
A cewar rahoton The Nation, Farfesa Yakubu ya bayyana cewa, bayan kammala shari'a, kotuna sun umarci hukumar da ta sake gudanar da zaɓuka a mazaɓu 34 na tarayya da na jihohi.
Kujerun sun haɗa da ta sanata guda ɗaya, ƴan majalisar wakilai 11 da ƴan majalisar dokoki na jiha 22.
Bugu da ƙari, ya yi nuni da cewa, za a gudanar da zaɓen cike gurbi biyo bayan murabus ko rasuwan mambobin, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Ya ce za a fitar da sahihin ranar gudanar da zaɓen da cikakken jaddawalin a ƙarshen ganawa da shugabannin jam’iyyar.
Jega Ya Kawo Hanyar Gyara Zaɓe a Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya kawo hanyoyin da za a gyara zaɓe a Najeriya.
Jega ya bayar da shawarar a kacancana hukumar INEC tare da haramta sauya sheƙar da ƴan siyasa suke yi a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng