Shugaban Majalisar Dattawa: Tsoffin Sanatocin APC Sun Roki Kalu, Yari Da Sauransu Su Janye
- An roki tsohon babban mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu da ya janye daga kudirinsa na son zama shugaban majalisar dattawa
- An kuma roki tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'Aziz Yari ya janye daga takarar sannan ya marawa zabin APC, Sanata Godswill Akpabio baya
- Tsoffin Sanatocin APC na jumhuriya ta daya zuwa ta hudu ne suka yi wannan roko a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni
Abuja - Tsoffin sanatocin jam'iyyar APC daga jumhuriyya ta biyu zuwa ta hudu sun bukaci Sanata Orji Uzor Kalu, tsohon gwamna Abdul'aziz Yari da sauran masu takarar kujerar shugaban majalisar dattawa da su janye sannan su marawa zabin jam'iyyar baya.
Ku tuna cewa kwamitin uwar jam'iyyar APC ya lamuncewa Sanata Godswill Akpabio tare da samun goyon baya daga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar The Sun ta rahoto cewa, a wani taro da ya gudana a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni, tsoffin yan majalisar sun bayyana cewa hukuncin jam'iyya ya fi na kudirin mutum.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Cif Olusegun Osoba, Alhaji Tanko Yakasai, Ambasada Godknows Igali da Archbishop John Praise, da sauransu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban taron, Sanata Basheer Lado, ya kuma yi kira ga yan majalisa daga jam'iyyun adawa da ke neman kujerar da su hakura da takararsu don zaman lafiya, hadin kan jam'iyya da kuma tafiyar da gwamnatin Tinubu cikin kwanciyar hankali.
Jaridar The Nation ta nakalto Osoba wanda ya yi magana a taron yana cewa:
"Ina so na roke ku kan batutuwa biyu. Mu shirya wani tsarin kamun kafa mai karfi ta hanyar shirya wani taro na dukkanin masu neman mukamin shugaban majalisar dattawa ta 10 domin nuna masu dalilin da yasa ya kamata su bi tsarin jam'iyyar.
"Jam'iyyar ta yanke shawarar raba mukami kuma ta mika mukamin ga wani bangare. Ba za mu so fara wannan gwamnati da wani rikici ba. Dama dai rikicin cire tallafin man fetur na nan a kasa."
Cire tallafin mai, Wike ya goyi bayan Shugaban kasa Tinubu
A wani labari na daban, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya goyi bayan shugaban kasa Bola Tinubu kan cire tallafin man fetur.
Wike ya ce idan har ana son ciyar da Najeriya gaba, toh dole sai an dauki wasu tsauraran matakai.
Asali: Legit.ng