Ganduje Na Yi Wa Tsarin Mika Mulki Kafar Ungulu, Kwamitin Karbar Mulki Na Abba Gida-Gida

Ganduje Na Yi Wa Tsarin Mika Mulki Kafar Ungulu, Kwamitin Karbar Mulki Na Abba Gida-Gida

  • Kwamitin karbar mulki na gwamnan jihar Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf ya zargi gwamnatin Ganduje da zagon kasa
  • Shugaban kwamitin, Abdullahi Baffa ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje na jan kafa wajen gudanar da shirye-shiryen mika mulki
  • Gwamnatin jihar ta karyata wannan zargin inda ta ce sam babu kamshin gaskiya a ciki
  • Ta ce laifin na kwamitin karbar mulkin ne da ya ki gabatar da sunayen wakilai uku kamar yadda gwamnatin ta bukata

Kano - Kwamitin karbar mulki na zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi zargin cewa gwamnati mai barin gado ta Abdullahi Umar Ganduje na yi wa shirinsu na karbar mulki zagon kasa, Daily trust ta rahoto.

Sai dai kuma, gwamnatin jihar ta ce babu kamshin gaskiya a zargin, tana mai ikirarin cewa kwamitin NNPP ya ki gabatar da sunayen mutane uku da kwamitin mika mulki na gwamnatin ya nema.

Kara karanta wannan

Ana wata: Likitoci za su tafi yajin aiki idan Buhari bai biya musu bukatunsu 2 ba

Ta ce duk da wannan, dukkanin ma'aikatu da hukumomin gwamnati suna ta gudanar da tsare-tsaren mika mulkin.

Gwamna Abdullahi Ganduje da Abba Kabir Yusuf
Ganduje Na Yi Wa Tsarin Mika Mulki Kafar Ungulu, Kwamitin Karbar Mulki Na Abba Gida-Gida Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a ranar Juma'a, shugaban kwamitin karbar mulki na zababben gwamna, Abdullahi Baffa ya ce dagewar da gwamnatin tayi na cewa dole sai sun zabi mutum uku su hadu da mutum 17 na kwamitin mika mulki na gwamnati ba daidai bane.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, ba zai yiwu ace sai sun hada kwamiti ba domin dai abu ne da ya shafi jam'iyyu biyu masu manufofi daban-daban.

Ya ce saboda dagewar da kwamitin karbar mulki ya yi na cewar "dole a yi abun da ya dace, Ganduje na ta jan kafa da yi wa tsarin mika mulkin zagon kasa: Har yanzu bai kaddamar da tawagar gwamnati ba bayan sanar da kafa ta kusan makonni hudu da suka wuce (abun bakin ciki, tawagar gwamnatin sun ce ba za su iya yin kowani zama da mu ba har sai gwamnati ta kaddamar da su."

Kara karanta wannan

Kano: "Mun Shirya Tsaf" Gwamna Ganduje Ya Maida Martani Ga Tsagin Abba Gida-Gida

Baffa ya ce don tabbatar da kammala tsarin mika mulki cikin nasara kafin ranar 29 ga watan Mayu, kwamitin karbar mulkin zai tattauna da manyan sakatarori, shugabannin hukumomin gwamnati da shugabanin ma'aiktan na kananan hukumomi 44 daga ranar 2 ga watan Mayu.

Gwamnatin Kano ta yi martani

Da yake martani ga zargin kwamitin karbar mulkin, kwamishinan labarai da harkokin cikin gida na jihar, Muhammad Garba, wanda ya kasance mamba a kwamitin mika mulki, ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a zargin.

Garba ya ce zuwa yanzu kwamitin karbar mulkin ya ki mika sunayen mutane uku da za su hadu da kwamitin mai mambobi 17, yana mai cewa an baiwa kwamitin karbar mulkin kujeru uku ne saboda tarin ayyukan da gwamnati za ta aiwatar a lokacin mika mulkin.

Ya kuma ce ba gaskiya bane cewa kwamitin baya aiki saboda gwamnan bai riga ya kaddamar da shi ba a hukumance, cewa akalla an yi zama biyu kuma shugaban kwamitin ya baiwa dukkanin ma'aikatu da hukumomin gwamnati umurnin kammala tsarin muka mulkinsu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Ganduje Ta Biya Muhuyi Rimin Gado Hakkokinsa, An Fara Kashe Kudin Wajen Aiwatar Da Muhimman Ayyuka

Ya ce tuni wasu daga cikin ma’aikatun suka kammala aikin mika bayanan da suka shafi ma'aikatunsu kuma da zaran kwamitin karbar mulkin ya mika sunayen wakilansa ga kwamitin za a tafi da su, rahoton Aminiya.

Ka kammala ayyukan da na faro ban gama ba, Ganduje ga zababben gwamnan Kano

A wani labarin, mun ji a baya cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya roki Abba Kabir Yusuf da ya yi kokari ya kammala ayyukan da gwamnatinsa ta faro amma bata kai ga gamawa ba don amfanin al'ummar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: