Da Dumi-Dumi: An Kori Mataimakin Shugaban APC a Jihar Edo Da Wasu Bakwai
- Jam'iyyar APC ta fatattaki wasu daga cikin manyan jiga-jiganta a jihar Edo saboda zargin cin amana
- APC ta kori mataimakin shugabanta, Francis Inegbeniki da wasu mambobin jam'iyyar bakwai kan zargin cewa sun yi wani taro na sirri
- Ana ganin sun yi wa jam'iyyun adawa aiki a lokacin zabe wanda ya kai ga kayen da jam'iyyar ta sha
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC)a jihar Edo ta kori mataimakin shugabanta, Francis Inegbeniki, tare da wasu mambobi bakwai daga karamar hukumar Esan ta tsakiya.
Labarin korar jiga-jigan na APC yana kunshe ne a cikin wata wasika dauke da sa hannun Rawlings Ekeoba, shugaban APC a karamar hukumar Esan da wasu 24, jaridar Tribune ta rahoto.
Ekeoba da sauransu sun aika wasikar zuwa ga shugaban APC a jihar Edo, Col. David Imuse (mai ritaya).
Laifin da korarrun 'ya'yan jam'iyyar suka aikata
A cewar wasikar, an zargi mambobin da abun ya shafa da yin taron sirri a wani otel da ke Eidenu Irrua gabannin zaben majalisar wakilai da na jiha wanda aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Yayin da wasu daga cikinsu ke yi wa jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP aiki, wasun su na yi wa Labour Party aiki don tabbatar da ganin cewa yan takararsu sun sha kaye a zaben."
A wasikar, an kuma bayyana cewa shugaban na APC a karamar hukumar Esan ya hadu da mambobi da masu ruwa da tsaki a ranar 20 ga watan Maris don bayyana dalilin da yasa jam'iyyar ta fadi a lokacin zaben.
An tattaro cewa an kafa kwamitin mutum biyar domin binciken mambobin jam'iyyar da aka kora saboda cin dunduniyar jam'iyya da dama.
Wasikar ta kara da cewar mutum daya a cikinsu, , Theophilus Okoh na gudunma ta daya ne kawai ya gurfana a gaban kwamitin don karyata batun kasancewarsa da hannu a zargin cin amanar jam'iyyar.
Tsohon dan takarar shugaban kasa ya nemi a dakatar da rantsar da Tinubu
A wani labari na daban, wani tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Ambrose Owuru, ya shigar da kara kotu inda ya nemi a dakatar da rantsar da Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.
A cewar Owuru, shine ya lashe zaben shugaban kasa a 2019 amma kuma bai ci wa'adinsa ba saboda an yi masa fin karfi,
Asali: Legit.ng