Idris Wase Da Jerin Yan Majalisa 8 Da Ke Son Zama Kakakin Majalisar Wakilai Na Gaba

Idris Wase Da Jerin Yan Majalisa 8 Da Ke Son Zama Kakakin Majalisar Wakilai Na Gaba

Fafutukar wanda zai gaji kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, na kara zafi gabannin zaben cike gurbi na ranar 15 ga watan Afrilu.

Yayin da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) bata riga ta yanke shawara ba kan yankin da za a mikawa kujerar, manyan yan takarar kujerar majalisar sun fara kamfen a bangarori daban-daban.

Yan majalisar wakilai a taro
Idris Wase Da Jerin Yan Majalisa 8 Da Ke Son Zama Kakakin Majalisar Wakilai Na Gaba Hoto: @femigbaja
Asali: Twitter

Shugaban majalisar wakilan mai barin gado, Hon. Femi Gbajabiamila ya yi jagoranci mafi zaman lafiya da diflomasiyya wanda ya fito da kyawun tsarin damokradiyya.

A wannan zauren, Legit.ng ta tattaro jerin sunayen manyan zababbun yan majalisa da ke neman kujerar kakakin majalisar wakilai na gaba.

Sun hada da:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

1. Mataimakin kakakin majalisar wakilai Idris Wase (APC, Plateau)

Kara karanta wannan

Zaben Cike Gurbi Na 2023: Jerin Manyan Yan Takara Da Kallo Ke Kansu

Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Wase
Idris Wase Da Jerin Yan Majalisa 8 Da Ke Son Zama Kakakin Majalisar Wakilai Na Gaba Hoto: : Hon Ahmed Idris Wase
Asali: Facebook

Ahmed Idris Wase ya kasance dan siyawa wanda ke rike da mukamin mataimakin kakakin majalisar wakilai a majalisa ta 9. Ya kasance dan jam'iyyar All Progressive Congress.

Dan majalisar tarayyar wanda ya nunawa al'ummar mazabarsa cewa ana iya samun shugabanci da wakilci nagari ya mayar da hankali wajen inganta rayuwar al'ummarsa ta hanyar bayar da fifiko kan ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi masu kyau da ruwa.

An zabi Hon. Ahmed Wase a matsayin mataimakin kakakin majalisa a majalisa ta 9, da kuri'u 358 ba tare da abokin hamayya ba.

2. Hon Yusuf Adamu Gagdi (APC, Plateau)

Dan majalisar wakilai, Hon Yusuf Adamu Gagdi
Idris Wase Da Jerin Yan Majalisa 8 Da Ke Son Zama Kakakin Majalisar Wakilai Na Gaba Hoto: Hon Yusuf Adamu Gagdi
Asali: Facebook

Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan sojojin ruwa, Hon. Yusuf Adamu Gagdi (APC, Plateau), shima ya shiga tseren masu son su gaji Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilai na 10.

An tattaro cewa Hon Gagdi, mai wakiltan mazabar Panskhin/Kanke/Kanam ta jihar Plateau yana ta ganawa da yan majalisa don tallata kansa ko da an turo kujerar kakakin majalisar zuwa yankin arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Akwai Yiwuwar ‘Dan Arewa Ya Gaji Gbajabiamilla, Ya Zama Shugaban Majalisar Tarayya

3. Muktar Betara (APC, Borno)

Dan majalisar wakilai daga Borno, Muktar Betara
Idris Wase Da Jerin Yan Majalisa 8 Da Ke Son Zama Kakakin Majalisar Wakilai Na Gaba Hoto: Ismail Aliyu Betara
Asali: Facebook

Rt. Hon. Aliyu Muktar Betara Aliyu OON, ya kasance dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Biu, Bayo, Kwaya Kusar, Shani ta jihar Borno.

Ko da dai sunansa bai shahara ba a matsayin dan majalisar tarayya, yana bayar da gagarumin gudunmawa wanda ke da matukar tasiri a kan mutanen jiharsa.

Ya shafe fiye da shekaru 14 yana wakiltan mazabarsa kuma har yanzu ana damawa da shi amma zai fafata da zababbun yan majalisa don gaje Gbajabiamila a majalisa ta 10.

4. Benjamin Kalu (APC, Abia)

Benjamin Kalu, mai magana da yawun majalisar wakilai, ya ce yana sha'awar son zama kakakin majalisar wakilai na 10.

Kalu ya ce ya cancanci jagorantar majalisar tarayyar, yana mai cewa ba a taba samun kakakin majalisa daga kudu maso gabas ba tsawon shekaru 40.

5. Sada Soli Jibiya (APC, Katsina)

Dan majalisar wakilai daga Katsina, Sada Soli Jibiya
Idris Wase Da Jerin Yan Majalisa 8 Da Ke Son Zama Kakakin Majalisar Wakilai Na Gaba Hoto: Sadauki Jibia
Asali: Facebook

Hon Sada Soli ya kasance dan siyasar Najeriya a matakin majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Fitattun Sanatocin Arewa 5 Da Ke Neman Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Yanzu haka Sada Jibiya na rike da mukamin dan majalisa mai wakiltan mazabar Jibia/Kaita a majalisar wakilai ta tara.

An sake zabar Hon. Soli a majalisar wakilai ta 10 don wakiltan mutanen Kaita/Jibia na jihar Katsina karkashin inuwar jam'iyyar APC.

6.Tunji Olawuyi (APC, Kwara)

Dan majalisar wakilai daga Kwara, Tunji Olawuyi
Idris Wase Da Jerin Yan Majalisa 8 Da Ke Son Zama Kakakin Majalisar Wakilai Na Gaba Hoto: Tunji Olawuyi
Asali: Facebook

Tunji Olawuyi, dan majalisa mai wakiltan mazabar Ekiti, Isin, Irepodun da Oke-Ero ta jihar Kwara ya fara kamfen din zarcewarsa a Oro, karamar hukumar Irepodun ta jihar Kwara yayin da fafutukar neman kujerar kakakin majalisa ke kara karfi.

Olawuyi shine zababben dan takarar jam'iyyar APC na mazabar Ekiti, Irepodun, Isin da Oke-ero ta Kwara a zaben fidda gwanin da aka yi a watan Yuni.

7. Hon. Makki Abubakar (APC, Jigawa)

Dan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Makki Abubakar
Idris Wase Da Jerin Yan Majalisa 8 Da Ke Son Zama Kakakin Majalisar Wakilai Na Gaba Hoto:Makki Abubakar
Asali: Facebook

Hon. (Dr) Makki Abubakar Yalleman wanda shine mataimakin shugaban kwamitin majalisar wakilai kan tsaro kuma dan majalisa mai wakiltan mazabar Mallammadori/Kaugama ta jihar Jigawa yana cikin masu tseren kujerar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Zababben Dan Majalisar Dokokin Jihar Borno Mai Wakiltar Chibok, Ya Rasu

8.Tajudeen Abbas (APC, Kaduna)

Dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna, Tajudeen Abbas
Idris Wase Da Jerin Yan Majalisa 8 Da Ke Son Zama Kakakin Majalisar Wakilai Na Gaba Hoto: Tajudeen Abbas
Asali: Facebook

Hon. Tajudeen Abbas, dan majalisa mai wakitan mazabar Zaria karkashin inuwa jam'iyyar APC yana da abubuwan da ake bukata don gaje Hon. Femi Gbajabiamila.

Babban dan majalisar ya kasance mutum mai matukar mutunci kuma takwarorinsa yan majalisa sun yarda da shi sosai.

Zai fafata da takwarorinsa takwas wajen neman kujerar kakakin majalisar wakilai na gaba.

9. Aminu Jaji (APC, Zamfara)

Hon. Aminu Sani Jaji
Idris Wase Da Jerin Yan Majalisa 8 Da Ke Son Zama Kakakin Majalisar Wakilai Na Gaba Hoto: Hon. Aminu Sani Jaji
Asali: Facebook

Daga cikin zababbun yan majalisar da ke neman kujerar kakakin majalisar wakilai, harda Rt. Hon. Dr. Aminu Sani Jaji.

Hon. Dr. Aminu Jaji, wanda aka fi sani da Garkuwan Matasan Arewa, ya kasance mutum mai tawali'u, kwazo, kwarewa, gogewa da dattako.

A yau, yana cikin yan siyasa mafi shahara kuma wanda ake ganin mutuncinsu a jihar Zamfara.

A wani labari na daban, zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya zargin Gwamna Abdullahi Ganduje da ware miliyoyin naira domin daukar nauyin yan daba da za su tarwatsa zaben cike gurbi na ranar Asabar, 15 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng