“Babu Wanda Zai Iya Korata Daga Najeriya”: Peter Obi Ya Magantu Bayan Badakalar UK
- Peter Obi, dan takarar jam'iyyar Labour Party a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu ya jaddada cewa babu mai tursasa masa barin kasar
- Da yake magana kan kama shi da aka yi a kasar Ingila, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce ya jajirce don fitar da Najeriya daga hannun barayi
- Ya kuma bayyana cewa ba zai hakura da kudirinsa ba har sai mutanen da ya dauka a matsayin barayi sun bar mukaman shugabanci a Najeriya
Anambra - Peter Obi, dan takarar jam'iyyar Labour Party a zaben shugaban kasa da aka kammala kwanan nan, ya dage cewa babu wanda zai iya tilasta masa barin Najeriya.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya kara da cewar jam'iyyarsa ta jajirce wajen farfado da kasar, yana mai cewa akwai "barayi" da yawa wadanda sune suka jefa al'ummar Najeriya a kangin wahala, Vanguard ta rahoto.
Rahoto: Yadda Yan 'Obidients' Suka Ceci Peter Obi a Filin Jirgin Sama Ana Tsaka Da Zarginsa Da Yin Basaja
Abun da Peter Obi ya ce game da tsare shi da aka yi a UK
Ya kuma sha alwashin cewa jam'iyyar Labour Party ta jajirce don fitar da irin wadannan mutane daga tsarin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya kuma yi alkawarin cewa ba zai yanke kauna da Najeriya ba har sai an fitar da irin wadannan mutane daga mukaman siyasar Najeriya, rahoton Daily Post.
Wani bangare na jawabinsa na cewa:
"Ana shan wahala sosai a kasar nan, shine abun da mu da muke Labour Party muke yaki don kawo karshensa. Akwai barayi da yawa a kasar nan. Don haka, jam'iyyar Labour Party ke yaki don samar da Najeriya sabuwa. Ina nan tare da ku, babu wanda zai tilasta mani barin Najeriya."
Peter Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a Onitsha a ranar Alhamis, 13 ga wayan Afrilu, inda ya bukaci mutanen mazabar Ogbaru da su fito sannan su zabi Labour Party a zaben cike gurbi na ranar Asabar, 15 ga watan Afrilu.
Ya koka cewa yan Najeriya na cikin mawuyacin hali kuma cewa wahalar da ake sha a kasar nan ta yi yawa.
A baya mun kawo cewa jami'an hukumar kula da shige da fice na kasar Ingila sun tsare Peter Obi a filin jirgin sama da ke birnin Landan kan zargin yin basaja.
Asali: Legit.ng