Yanzu Yanzu: Yan Daba Sun Karbe Tare Da Kona Kayan Zabe a Bayelsa
- Yan bindiga sun karbe tare da kona kayan zabe a mazabar Ogbia da ke jihar Bayelsa
- Jami’an hukumar zabe da aka tura yankin sun juya zuwa Yenagoa domin tsiratar da ransu
- Zaben yan majalisar jiha na gudana a fadin Bayelsa kasancewar sai a watan Nuwamba za a yi zaben gwamnan jihar
Bayelsa - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wasu bata gari sun kwace tare da kona kayayyakin zabe a gudunma uku a mazabar Ogbia da ke jihar Bayelsa yayin zaben majalisar jiha da ke gudana a jihar.
Tuni jami'an hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da aka tura mazabar suka fara komawa Yenagoa don tsira da rayuwarsu yayin da yan daba suka mamaye yankin.
An tattaro cewa magoya bayan jam'iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da na All Progressives Congress (APC) suna fafatawa a kujerar majalisar dokokin.
Jam'iyyun na fafutukar ganin sun zama masu rinjaye a majalisar dokokin jihar gaba gabannin zaben gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hukumar INEC ta yi martani kan lamarin
Kakakin INEC a jihar Bayelsa, Mista Wilfred Ifogah, wanda ya tabbatar da lamarin ga jaridar Daily Trust ya ce, hukumar za ta fitar da sanarwa game da lamarin nan gaba.
Ya ce:
"Mun samu rahoton cewa an kwace kayayyakin da ya kamata ayi zaben majalisar jiha da shi a gudunma biyu ko uku a mazabar Ogbia sannan aka kona su, watakila za mu bayar da sanarwa nan gaba kan lamarin."
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, alamu sun nuna ba za a yi zabe ba a mazabar Ogbia 2, kasancewar jami'an INEC sun rigada sun dauki hanyar komawa Yenagoa.
A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar yan sanda ta yi kakkausan gargadi ga masu shirin tayar da zaune tsaye yayin zaben gwamnoni da na yan majalisar jiha da za a yi a ranar Asabar, 18 ga watan Maris.
Rundunar yan sandan ta ce duk mai shirin mutuwa ya fito da sunan kwace akwatunan zabe ko kuma kawo hargitsi da yunkurin hana mutane gudanar da hakkinsu na kada kuri'a a yayin zaben na yau Asabar.
Asali: Legit.ng