Atiku Ya Lissafa Lauyoyi Manya 19 Da Zasu Tsaya Masa a Kotun Zabe

Atiku Ya Lissafa Lauyoyi Manya 19 Da Zasu Tsaya Masa a Kotun Zabe

  • Yayinda ake shirin zuwa kotun zabe, Atiku ya bayyana lauyoyi goma sha tara da zasu tsaya masa
  • Dan siyasan ya zabi manyan lauyoyi masu mukamin 'SAN' domin su kwato masa hakkinsa
  • Ya jaddada cewa shi da Okowa yan Najeriya suka zaba ranar zaben 25 ga watan Febrairu, 2023

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takara shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zabi manyan lauyoyi 19 da zasu wakilcesa a kotun zaben shugaban kasa.

Atiku ya tattauna da wadannan manyan lauyoyin ne a hedkwatan yakin neman zabensa dake Abuja ranar Laraba, rahoton TheCable.

Ya bukacesu su tabbatar da cewa an tafka rashin gaskiya da bin tsarin doka wajen gudanar da zaben shugaban kasar 25 ga watan Febrairu, 2023.

Atiku
Atiku Ya Lissafa Lauyoyi Manya 19 Hoto: Atiku
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Da duminsa: Ana Saura Kasa Da Kwana 3 Zabe, Shugabar Matan PDP a Sokoto Ta Koma APC

A riwayar PremiumTimes, Atiku ya bayyana musu cewa bayan son a kwato masa hakkinsa da aka kwace masa saboda shi yan Najeriya suka zabe, yana son lauyoyin suyi amfani da wannan lamari wajen karfafa demkradiyya a Najeriya.

Lauyoyin guda 19 masu mukamin SAN karkashin jagorancin JK Gadzama.

Ga jerinsu:

Chris Uche (SAN),

Paul Usoro (SAN),

Tayo Jegede (SAN),

Ken Mozia (SAN),

Mike Ozekhome (SAN),

Mahmood Magaji (SAN),

Joe Abraham (SAN),

Chukwuma Umeh (SAN),

Garba Tetengi (SAN)

Emeka Etiaba (SAN).

Goddy Uche (SAN),

Prof. Maxwell Gidado (SAN);

A. K. Ajibade (SAN),

O. M. Atoyebi, (SAN),

Nella Rabana (SAN),

Paul Ogbole (SAN),

Nuremi Jimoh (SAN),

Abdul Ibrahim (SAN).

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida