Tsohon Gwamna Ya Ci Amanar APC, Yana Tallata ‘Dan Takarar Jam’iyyar Adawa Karara
- Ibikunle Amosun ya dage sai an hana Dapo Abiodun zarcewa a matsayin Gwamnan jihar Ogun
- Yadda ya yake shi a 2019, ‘Dan siyasar ya dage dole sai an yi waje da Gwamna Abiodun a zaben 2023
- A cewar Amosun murdiya aka yi har APC ta iya lashe zaben da aka yi a lokacin da zai bar karagar mulki
Ogun - Ibikunle Amosun wanda Sanata a karkashin Jam’iyyar APC, ya halarci taron ‘dan takarar ADC a zaben Gwamnan jihar Ogun a zaben bana.
Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Laraba cewa Ibikunle Amosun bai tare da Dapo Abiodun.
A maimakon a ga Sanata Ibikunle Amosun yana taya Gwamna Dapo Abiodun yakin neman zaben tazarce, sai ga shi yana goyon bayan 'yan adawa.
Dapo Abiodun ne ya gaji Ibikunle Amosun a Mayun 2023 a karkashin jam’iyyar APC da ya yi mulki, amma babu jituwa tsakaninsa da magajin shi.
Kasa Otegbeye, Sama Tinubu
A zaben Gwamna da za ayi a watan Maris, tsohon Gwamnan na Ogun zai goyi bayan Biyi Otegbeye na ADC ya doke jam’iyya mai mulki watau APC.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amma a zaben shugaban kasa, Sanatan na Ogun ta tsakiya yana cikin wadanda ke goyon bayan Bola Ahmed Tinubu ya karbi shugabancin Najeriya.
Amosun zai yi wake da shinkafa
Amosun ya janye neman takarar shugaban kasarsa, ya goyi bayan Bola Tinubu a zaben fitar da gwani, amma a gida bai tare da ‘dan takaransu na APC.
Daily Post ta ce kwatsam aka ga ‘Dan majalisar a wajen taron kaddamar da yakin neman zaben Gwamna na ADC a fadar Ake da ke birnin Abeokuta.
Rahoton ya ce an ga shi yau da karfe 1:49 wajen gangamin da ‘yan jam’iyyar ADC suka shirya.
Zuwan Amosun wanda ya yi Gwamna sau biyu a Ogun ya farantawa mabiyansa da ‘yan jam’iyyar hamayya ta ADC rai a wajen yawon kamfen da ake yi.
Leadership ta ce tsohon Gwamnan ya soki Gwamnati mai-ci, sannan ya jagoranci tawaga zuwa fadar Mai martaba Sarkin Egba, Adedotun Gbadebo.
Ya APC za ta yi da Ibikunle Amosun?
Tun a baya an ji labari Ibikunle Amosun wanda ya yi mulki tsakanin 2011 zuwa 2019 ba zai marawa magajinsa da ke takara jam’iyyarsa baya a zabe ba.
A zaben da ya wuce, Sanata Amosun ya goyi bayan Adekunle Akinlade na APM, daga baya sai aka ji ‘dan siyasar ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Asali: Legit.ng